Da Dumi-Dumi: Mutum 14 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Sake Kai Hari Jihar Kaduna

Da Dumi-Dumi: Mutum 14 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Sake Kai Hari Jihar Kaduna

  • Wasu yan bindiga sun sake kai hari Kudancin Kaduna, inda suka kashe akalla mutum 14 tare da kone wasu gidaje
  • A wani harin ɗaukar fansa, wasu mutane sun kona wata Rugar Fulani baki ɗaya
  • Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Jalige, ya tabbatar da kai harin biyu, yace mutane su daina ɗaukar doka a hannun su

Kaduna - Akalla mutum 14 suka rasa rayukansu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Mado, karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Maharan sun kone wasu gidaje da dama yayin da suka kai harin ranar Asabar da daddare.

Da yake zantawa da Dailytrust, shugaban kwamitin tsaro na yankin Aytap, Mista John Bala Gora, ya yi mamakin yawaitar hare-haren duk da kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwanda aikin tukin Keke Napep da koyarwa: Malamar makaranta ta ajiye karantarwa

Gora ya sake kira ga jami'an tsaro su kara zage dantse wajen kare al'umma da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

Yan bindiga sun kashe mutum 14 a Kaduna
Da Dumi-Dumi: Mutum 14 Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Sake Kai Hari Jihar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kona rugar fulani

A wani harin daukar fansa, wasu mutane sun kone wata rugar fulani a Kankada, yankin Madakiya, karamar hukumar Zangon Kataf da sanyin safiyar Lahadi.

Daya daga cikin mazaunan rugar da aka taba, Halima Haruna, wacce aka kubutar kuma aka kaita caji ofis na Zonkwa, tace maharan sun zagaye rugarsu da safiyar Lahadi.

Matar shugaban fulanin Kankada, Haruna, tace ta ga gawar mutum biyu, mace da namiji, yayin da take neman wurin ɓuya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Tace:

"Dole ta sa muka gudu muka ɓuya yayin da wasu daga cikin mutanen rugar suka tsere cikin jeji domin ceton rayuwarsu."
"Bamu san meyafaru da su ba yanzun, mun shafe awa 3 kafin jami'an tsaro su zo su ɗauke mu zuwa caji ofis ɗin Zonkwa. Sun kone mana gidajen mu baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Allah ya yadda: Hotunan Jarumi kuma mawaki Garzali Miko tare da zukekiyar matarsa

"Maharan sun faɗa mana sun zo ɗaukar fansa ne kan harin da aka kai musi ranar Asabar da daddare, wanda mu bamu san komai ba."

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Da yake tabbatar da harin guda biyu, Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, yace an tura jami'an yan sanda yankunan da abun ya shafa.

Ya yi kira ga mutanen Zangon Kataf, da kuma kudancin Kaduna baki ɗaya, su daina ɗaukar doka a hannun su.

A wani labarin kuma Gwamna Lalong Ya Roki Al'umma Yafiya Kan Kisan Gillan da Aka Yi Wa Musulmai a Jos

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, ya roki gwamnati da kuma al'ummar jihar Ondo yafiya bayan kisan gillan da aka yiwa mutanensu a Jos.

Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa a ranar 14 ga watan Agusta aka kashe matafiya 23 yan jihar Ondo yayin da hanya ta biyo da su Jos.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki N500,000

Asali: Legit.ng

Online view pixel