Bidiyoyi: An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki N500,000

Bidiyoyi: An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki N500,000

  • Alkawari ya cika, burin masoya ya tabbata, an daura auren Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero
  • Garin Bichi dake jihar Kano ya cika makil da manyan mutane na fadin kasar nan har da kasashen ketare domin daurin auren
  • Ministoci, gwamnoni, fitattun 'yan siyasa da masu fadi a ji a kasar nan sun shaida daurin auren kan sadaki N500,000

Bichi, Kano - Allah ya yadda, alkawari kuma ya cika. An daura auren Yusuf Muhammadu Buhari, da daya tilo namiji na shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero, diyar mai martaba Sarki Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero.

Babu shakka garin Bichi dake jihar Kano ya cika dankam da jiga-jigai na fadin kasar nan har da kasashen ketare, wadanda suka dinga tururuwar zuwa shaida daurin auren.

Kara karanta wannan

Daurin auren Yusuf Buhari: Jiragen Alfarma fiye 25 ne suka dira a Kano, Ƴan Nigeria sunyi martani

Hotuna da bidiyoyi: An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki 500,000
Hotuna da bidiyoyi: An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki 500,000. Hoto daga @buharisallau
Asali: Instagram

A hotuna da bidiyoyin da Legit.ng ta tattaro muku, an hango manyan 'yan siyasa da suka hada da gwamnoni, ministoci da fitattun 'yan siyasar kasar nan.

Ba a kasar nan kadai, Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Shugaba Bazoum Mohammed ya halarci wannan gagarumin daurin auren.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin daurin auren, rahotanni da hotuna da suka bayyana sun nuna yadda filin sauka da tashin jiragen sama na Kano ya cika makil da jiragen sama na masu fadi a ji da hamshakan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel