Gwamna Lalong Ya Roki Al'umma Yafiya Kan Kisan Gillan da Aka Yi Wa Musulmai a Jos

Gwamna Lalong Ya Roki Al'umma Yafiya Kan Kisan Gillan da Aka Yi Wa Musulmai a Jos

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya roki gwmanati da al'ummar Ondo yafiya kan kisan da ya faru a Jos
  • Gwamnan yace waɗanda suka aikata lamarin sun yi hakane domin wargaza zaman lafiyar da aka gina a jihar
  • Shugaban Fulani, Kabir Muhammed, yace sun hakura domin zaman lafiyar Najeriya

Plateau - Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, ya roki gwamnati da kuma al'ummar jihar Ondo yafiya bayan kisan gillan da aka yiwa mutanensu a Jos, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta ruwaito muku cewa a ranar 14 ga watan Agusta aka kashe matafiya 23 yan jihar Ondo yayin da hanya ta biyo da su Jos.

Hakanan kuma yayin lamarin, an jikkata wasu mutum 23 daga cikin matafiyan, waɗanda suka dawo daga wa'azin da suka halarta a Bauchi.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato
Gwamna Lalong Ya Roki Al'umma Yafiya Kan Kisan Gillan da Aka Yi Wa Musulmai a Jos Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Tawagar gwamnatin Filato ta je ta'aziyya Ondo

Gwamna Lalong ya nemi yafiya kan harin ta bakin mataimakinsa, Sonny Tyoden, wanda ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Ondo yin ta'aziyya, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mr Tyoden yace sun kawo wannan ziyarar ne domin yin ta'aziyya da kuma neman afuwar gwamnati da mutanen Filato daga iyalan mamatan da kuma al'ummar Ondo baki ɗaya.

Mataimakin gwamnan ya nemi yafiya kan kisan da wasu bara gurbi suka aikata, inda yace yan ta'addan sun yi haka ne don kashin kansu ba domin addini ba ko kabila.

Mista Tyoden yace:

"Gwamna Lalong ya damu matuka da faruwar lamarin, wanda aka aikata da nufin tada rikici domin wargaza zaman lafiyar da aka samu a jihar tun zuwan shi Ofis shekara 6 da suka gabata."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Sake Kashe Mutum 7 a Jos Bayan Kisan Gillan da Akai Wa Musulmai

"Muna tabbatar da cewa gwamnati zata cigaba da kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya baki ɗaya, kuma waɗanda suka aikata wannan abun zasu girbi abinda suka shuka."

Gwamnatin Filato ta ɗauki matakin da ya dace

A jawabinsa, gwamnan jihar Ondo, Akeredolu, ya yabawa gwamna Lalong bisa gaggauta ɗaukar matakai don magance abinda ka iya zuwa ya dawo.

Gwamnan wanda mataikinsa, Lucky Aiyedatiwa, ya wakilata yace gwamnan na samun labarin ya yi gaggawar zuwa kasuwar shanu domin jajantawa shugabannin Fulani.

Fulani sun hakura da abunda ya faru

Shugaban Fulani na yankin kudu maso yamma, Kabiru Muhammed, yace sun yafe abinda ya faru domin tabbatar zaman lafiya a Najeriya.

Ya yi alkawarin cewa babu wani harin ɗaukar fansa da za'a kai domim zaman lafiyar Najeriya ta fi bukatar ɗai-daikun mutane.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sako Daliban Makarantar Bethel Baptist Kaduna

Yan bindigan da suka sace ɗalibai a makarantar Bethel Baptist Kaduna sun sako karin dalibai 15.

Kara karanta wannan

Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamnan Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jiharsa

A baya dai barayin sun sako yara 28 daga cikin waɗanda suka sace bayan biyan miliyan N50m kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel