Allah ya yadda: Hotunan Jarumi kuma mawaki Garzali Miko tare da zukekiyar matarsa

Allah ya yadda: Hotunan Jarumi kuma mawaki Garzali Miko tare da zukekiyar matarsa

  • Jarumi kuma mawakin matashi a Kannywood, Garzali Miko ya angwance da rabin ransa
  • Alkawarin masoyan ya cika, an daura auren Garzali da Habiba ne a ranar Juma'a a garin Kaduna
  • Kamar yadda abokan aikinsa, 'yan uwa, masoya da abokan arziki suka dinga wallafawa, sun taya shi murnar wannan cigaban

Kaduna - Fitaccen jarumi kuma mawakin masana'antar Kannywood, Garzali Miko, ya angwance inda yayi wuff da zukekeiyar budurwa.

Matashin ya kasance mai baiwar waka da kuma wasan kwaikwayo duka da dai har yanzu za a iya cewa jarumi ne mai tasowa.

Allah ya yadda: Hotunan Jarumi kuma mawaki Garzali Miko tare da zukekiyar matarsa
Allah ya yadda: Hotunan Jarumi kuma mawaki Garzali Miko tare da zukekiyar matarsa. Hoto daga @Garzalimiko
Asali: Instagram

A ranar Juma'a da ta gabata ne aka daura auren jarumin kuma mawaki a garin Kaduna da masoyiyarsa mai suna Habiba.

Babu shakka abokan aikinsa, masoya, 'yan uwa da kuma abokan arziki sun dinga taya shi murna ta hanyar wallafa kyawawan hotunansa tare da amaryarsa Habiba jim kadan bayan daura aurensu.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Kaduna kan raba kudin fansa, sun kashe juna har mutum 9

Allah ya basu zaman lafiya tare da zuri'a dayyiba, Ameen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel