Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Jihar Zamfara

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Jihar Zamfara

  • Wasu miyagun yan bindiga sun kai hari kauyen Adabka dake jihar Zamfara ranar Asabar
  • Maharan sun kwashe fiye da wanni hudu a kauyen yayin harin, inda suka yi awon gaba da magajin garin
  • Wata majiya ta bayyana cewa a makon da ya gabata yan sandan dake yankin suka bar kauyen

Zamfara - Wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Adabka dake yankin karamar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Wata majiya daga yankin ya bayyana cewa maharan sun shiga kauyen ranar Asabar da misalin ƙarfe 12:00 na rana.

Majiyar ta kara da cewa yan bindigan sun ci karen su babu babbaka tun sanda suka shiga yankin har karfe 4:00 na yamma, inda suka yi awon gaba da magajin gari, Alhaji Nafi'u Shehu.

Alhaji Nafi'u Shehu
Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Jihar Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mutum nawa harin ya shafa?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin yace yan bindigan ba su kashe kowa ba yayin harin na tsawon awanni hudu.

Majiyar tace:

"Yan bindiga sun shiga ƙauyen tun karshe 12:00 na rana har karfe 4:00 na yamma, ba su kashe kowa ba amma sun sace magajin gari."

An janye jami'an yan sanda

Majiyar ta bayyana cewa a makon da ya gabata jami'an yan sanda dake yankin suka fice wanda hakan ya baiwa yan bindigan damar kawo harin.

Kauyen Adabka yana da nisan kilomita 165 daga cikin garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Har zuwa yanzun rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ba ta sanar da kai wannan harin a hukumance ba.

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Sheke Wani Kasurgumin Dan Fashi da Ake Nema Ruwa a Jallo

Rundunar yan sanda reshen jihar Imo ta bayyana cewa jami'an yan sanda sun bindige wani sanannen ɗan fashi da aka jima ana nema ruwa a jallo.

Kakakin yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, yace sanannen ɗan fashin mai suna, Bugatti, ya gamu da ajalinsa ne bayan jami'an sun gano maboyarsa a Nsu, karamar hukumar Mbano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel