Matasa a jihar Delta sun kona Masallaci kurmus don yan bindiga sun kashe shugaban yan banga

Matasa a jihar Delta sun kona Masallaci kurmus don yan bindiga sun kashe shugaban yan banga

  • Wasu sun fitittiki Musulmai daga cikin Masallaci sannan sun banka wuta
  • Wannan ya biyo bayan kisan da yan bindiga sukayiwa wani dan garin
  • Mutane garin ba tare da hujja ba na zargin yan Arewa da aikata laifin

Delta - Wasu fusatattun matasa a garin Jeddo, karamar hukumar Okpe ta jihar Delta sun Masallacin Musulmai kurmus don zanga-zangan kisan shugaban yan bangan yankin.

An ruwaito cewa yan bindiga sun hallaka shugaban yan bangan mai suna George Akiru, wanda akafi sani da Scosco.

Rahoton ya kara da cewa sai da matasan suka fitittiki Musulmai da yan Arewa daga cikin Masallacin kafin banka wuta ranar Juma'a, saboda suna zargin su suka kashe shi.

Kisan shugaban yan bangan ya tayar da kura a yankin inda matasan suka lashi takobin daukar fansa.

Wani matashi a yankin, Ubada Umokoro, ya bayyanawa manema labarai cewa,

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Kaduna kan raba kudin fansa, sun kashe juna har mutum 9

"Zamu dau fansa nan ba da dadewa ba saboda sun kashe babban dan asalin wannan gari."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an tsaro sun bazama Jeddo domin kwantar da kura.

DailyPost ta ce ta tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, inda ya tabbatar da aukuwan lamarin.

Yace an kaddamar da bincike kan lamarin.

Matasa a jihar Delta sun kona Masallaci kurmus
Hoto: Delta
Matasa a jihar Delta sun kona Masallaci kurmus don yan bindiga sun kashe shugaban yan banga
Asali: Twitter

Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, sun ce matasan Irigwe

A wani labarin daban, wasu yan bindiga da ake zargin matasan Irigwe ne sun kai wa Musulmai matafiya 90 hari a jihar Plateau ranar Asabar, akalla mutum 22 sun mutu, yan sanda suka tabbatar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya bayyana cewa wasu matasa Kirista yan garin Irigwe suka kaiwa Musulman farmaki.

Jami'in gwamnatin mai suna Danladi Atu wanda ya ziyarci asibitin da aka kai wadanda suka jikkata yace:

Kara karanta wannan

Muzaharar Ashura ta yan Shi'a ta rikide zuwa rikici a Sakkwato birnin Shehu

"Mutum 25 aka tabbatar yanzu sun mutum."

Hakazalika kungiyar Miyetti Allah MACBAN tace ta kirga gawawwaki 25. Wakilin Miyetti Allah, Malam Nura Abdullahi yace:

"Mun yiwa gawawwaki 25 wanka kuma muna shirin biznesu."

Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya yi Alla-wadai da wannan hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel