Gwarazan Yan Sanda Sun Sheke Wani Kasurgumin Dan Fashi da Ake Nema Ruwa a Jallo

Gwarazan Yan Sanda Sun Sheke Wani Kasurgumin Dan Fashi da Ake Nema Ruwa a Jallo

  • Rundunar yan sanda ta bayyana cewa jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka sanannen ɗan fashi a Imo
  • Kakakin yan sandan jihar, Mike Abattam, ya sanar da cewa jami'an bijilanti ne suka taimaka aka samu wannan nasarar
  • Yace an yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da tawagar yan fashin inda jami'an suka bindige shi

Imo - Rundunar yan sanda reshen jihar Imo ta bayyana cewa jami'an yan sanda sun bindige wani sanannen ɗan fashi da aka jima ana nema ruwa a jallo, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kakakin yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, yace sanannen ɗan fashin mai suna, Bugatti, ya gamu da ajalinsa ne bayan jami'an sun gano maboyarsa a Nsu, karamar hukumar Mbano.

Dailytrust ta ruwaito cewa Bugatti ya jima a wannan yankin yana aikata ayyukan ta'addancinsa a kan mutanen yankin.

Kara karanta wannan

Matasa a jihar Delta sun kona Masallaci kurmus don yan bindiga sun kashe shugaban yan banga

Yan sanda sun kashe sanannen ɗan fashi a Imo
Gwarazan Yan Sanda Sun Sheke Wani Kasurgumin Dan Fashi da Ake Nema Ruwa a Jallo Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Su wa suka taimaka wa yan sanda da bayanai?

A sanarwar da Abattam ya fitar ranar Asabar, yace yan sanda sun samu rahoto daga yan bijilantin yankin Nsu, ranar Jumu'a, inda suka tabbatar da sun ga ɗan fashin da wasu yaransa biyu.

Abattam yace:

"Kungiyar yan bijilanti dake yankin, wanda suke aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar yan sanda, sun yi gaggawar sanar da tawagar yan sandan sintiri na yankin."
"Nan take suka tafi zuwa wurin da wanda ake zargin da tawagarsa suke ɓuya a cikin daji, suna yin arba da jami'an tsaro sai aka fara musayar wuta."
"Yayin wannan artabu ne jami'an tsaro suka sami nasarar hallaka shugabansu, Bugatti, kuma suka kwato bindigar da yake amfani da ita yayin da sauran suka tsere."

A wani labarin kuma Sojoji Sun Gargadi Yan Shi'a Mabiya Sheikh Zakzaky Kan Shirin Fitowa Zanga-Zanga

Kara karanta wannan

Muzaharar Ashura ta yan Shi'a ta rikide zuwa rikici a Sakkwato birnin Shehu

Rundunar sojojin Najeriya ta yi kira ga mabiya akidar shi'a dake shirin zanga-zanga a Jos kada su kuskura su fito.

Sojojin sun ce duba da yanayin da ake ciki a jihar, ba zasu bari a gudanar da irin wannan ayyukan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262