Dalilin da Yasa Yan Ta'adda Ba Zasu Iya Kwace Najeriya Ba Kamar Afghanistan, Lai

Dalilin da Yasa Yan Ta'adda Ba Zasu Iya Kwace Najeriya Ba Kamar Afghanistan, Lai

  • Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammed, ya tafi kasar Amurka domin ganawa da manyan kafafen watsa labarai na aduniya
  • Ministan yace sam ba'a yiwa Najeriya adalci ba idan aka haɗa da matsalar tsaron da take ciki da na Afghanistan
  • Yace Najeriya ta samu nasarori a yakin da take da yan ta'adda cikin shekaru 6 da suka gabata

Abuja - Ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammed, yace Najeriya ba ta gaza ba kuma ba zata bi sahun Afghanistan ba, inda yan ta'adda suka kwace iko, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a Washington DC ta kasar Amurka yayin fira da kafafen watsa labarai na duniya da suka haɗa da BBC rediyo da talabijin, Bloomberg da Politico.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Shugaba Buhari Ke Zuwa Landan a Duba Lafiyarsa, FG

Ministan yaje kasar Amurka ne domin ganawa da manyan kafafen watsa labarai na duniya a kan nasarorin gwamnatin Buhari da kuma kokarin da take na magance matsalar tsaro.

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed
Dalilin da Yasa Yan Ta'adda Ba Zasu Iya Kwace Najeriya Ba Kamar Afghanistan, Lai Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da yake zantawa da NAN bayan taronsa da kafafen watsa labarai uku, Muhammed yace ba dai-dai bane a rika alakanta yanayin tsaron Najeriya da na Afghanistan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muna samun Nasarori a Najeriya

Ya jaddada cewa Najeriya tana samun nasara kan yan ta'adda kuma ba zata bi sahun Afghanistan ba, inda yan ta'adda suka kwace mulki.

Premium times ta ruwaito Lai Muhammed na cewa:

"Najeriya bata gaza ba kuma ba zata taba gazawa ba. Tabbas muna da kalubale sosai a wasu sassan ƙasa amma hakan ba yana nufin mun gaza bane."
"Kasar da ta gaza itace kasar da babu muhimman abubuwan rayuwa kuma Najeriya ba ta kai wannan matakin ba."

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Wajibi Sheikh Pantami Ya Yi Allah Wadai da Abinda Taliban Ta Yi a Afghanistan, HURIWA

Shin Najeriya ta afka cikin yaki?

Muhammed yace Najeriya bata tsunduma cikin yaki ba, inda ya kara da cewa ana amfani da labaran karya wajen kara jefa kasar cikin yanayi a idon duniya.

Ministan yace:

"Idan har abinda ya faru a Afghanistan shine zai cigaba, to kamata yayi a yabawa gwamnatin tarayya saboda yadda ta ɗauki mataki kan rashin tsaro a shekaru 6 da suka gabata."
"Darasin da muka ɗauka a halin da Afghanistan ta tsinci kanta a yau shine, sama da shekaru 20 da Amurka ta shigo cikin lamarin, ta kashe tiriliyoyin daloli, dubbannin yan Amurka sun mutu, amma cikin makwanni Taliban ta kwace iko."
"Ya kamata wannan ya zama darasi ga kowace kasa cewa idan kana yaki da matsalar tsaro ko wata kungiya mai tsattsauran ra'ayi, yana da wahala ka shawo kan matsalar."
"Ya zama wajibi ka kasance a shirye kuma ka yi amfani da duk wasu hanyoyi wajen shawo kan matsalar."

Kara karanta wannan

Har yanzu bamu kammala bincike kan Abba Kyari ba, Hukumar yan sanda

A wani labarin kuma An Tsaurara Tsaro a Bichi Yayin da Ake Shirye-Shiryen Bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero

Masarautar Bichi a jihar Ƙano ta cika da jami'an tsaro ta ko ina yayin da ake cigaba da shirye-shiryen ɗaura auren Yusuf, ɗa ɗaya tilo ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari , da amaryarsa Zahra, ɗiyar sarkin Bichi.

Shirye-shirye sun yi nisa domin ɗaura auren wanda aka tsara za'a gudanar a babban masallacin Jumu'a na Bichi da karfe 1:30 na ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel