An Tsaurara Tsaro a Bichi Yayin da Ake Shirye-Shiryen Bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero

An Tsaurara Tsaro a Bichi Yayin da Ake Shirye-Shiryen Bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero

  • Am jibge jami'an tsaro a fadar sarkin Bichi yayin da ake cigaba da shirye-shiryen bikin Yusuf Buhari
  • Shugaban kwamitin shirye-shirye, Madakin Bichi. Alhaji Nura Ahmad, yace an kammala duk wasu tsare-tsare
  • Yace za'a fara abubuwan da aka tsara daga ranar Alhamis, inda za'a fara da addu'a a babban masallacin Jumu'a

Bichi, Kano - Masarautar Bichi a jihar Ƙano ta cika da jami'an tsaro ta ko ina yayin da ake cigaba da shirye-shiryen ɗaura auren Yusuf, ɗa ɗaya tilo ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da amaryarsa Zahra, ɗiyar sarkin Bichi.

Shirye-shirye sun yi nisa domin ɗaura auren wanda aka tsara za'a gudanar a babban masallacin Jumu'a na Bichi da karfe 1:30 na ranar Jumu'a.

Madakin Bichi, Alhaji Nura Shehu Ahmad, wanda shine shugaban kwamitin shirye-shirye na bikin auren da kuma naɗin Alhaji Nasir Ado Bayero.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, Attajirai, da sauran manyan kasa za su je Bichi wajen auren ‘Dan Shugaban kasa

Ya shaidawa manema labarai cewa za'a fara gudanar da shagalin bikin da abubuwan da aka tsara ranar Alhamis, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yusuf Buhari da Zahra Bayero
An Tsaurara Tsaro a Bichi Yayin da Ake Shirye-Shiryen Bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero Hoto: @northern_hibiscuss
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanne abubuwa aka tsara yi a bikin?

A jawabin da yayi wa manema labarai madakin Bichi yace:

"Za'a fara da addu'a a babban masallacin jumu'a na garin Bichi da misalin karfe 3:30 na rana."
"Bayan nan kuma za'a gudanar da lakca a kwalejin ilimi ta tarayya FCE Bichi da karfe 4:00 na yamma."

Wane shiri ka yi na tsaro?

Alhaji Ahmad yace kwamitin tsaro a wurin bikin bisa jagorancin tsohon kwamishinan yan sanda, Shehu Kabiru Bayero, ya kammala duk shirin da ya kamata.

Jami'an tsaron sun haɗa da, yan sandan farin kaya (DSS), jami'an hukumar NSCDC, yan Hisbah, da yan Bijilanti.

Hakanan kuma yace an sake tada wani karamin kwamiti wanda ya kunshi ma'aikatan lafiya, waɗanda zasu tabbatar an bi ka'idojin kariya daga yaɗuwar cutar COVID19.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Saka Ranar Gangamin Tarukanta Na Kananan Hukumomi

Jam'iyyar APC mai mulki ta sanya ranar 4 ga watan Satumba domin gudanar da gangamin tarukanta na jihohi, kamar yadda punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da APC ta fitar ranar Laraba a Abuja ɗauke da sa hannun sakarenta.

A kwanakin bayane APC ta gudanar da zabukan shugabanninta a matakin gunduma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262