Dalilin da Yasa Shugaba Buhari Ke Zuwa Landan a Duba Lafiyarsa, FG

Dalilin da Yasa Shugaba Buhari Ke Zuwa Landan a Duba Lafiyarsa, FG

  • Ministan yada labarai, Lai Muhammed, ya bayyana cewa ba Buhari bane shugaba na farko dake fita kasar waje duba lafiya
  • A cewarsa idan kana da likitan da ka amince da shi shekara 30 da suka gabata babu dalilin canza shi
  • Muhammed, yace kowane shugaba yana da damar zaɓan wanda ya amince da shi ya duba lafiyarsa

Abuja - Ministan yaɗa labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace fita kasar waje duba lafiya da shugaba Buhari ke yi ba yana nufin ɓangaren lafiya a Najeriya ya lalace bane, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a Washington DC ta kasar Amurka yayin fira da kafafen watsa labarai na duniya da suka haɗa da BBC rediyo da talabijin, Bloomberg da Politico.

Ministan yaje kasar Amurka ne domin ganawa da manyan kafafen watsa labarai na duniya a kan nasarorin gwamnatin Buhari da kuma kokarin da take na magance matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

Ministan yaɗa labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed
Dalilin da Yasa Shugaba Buhari Yake Zuwa Landan a Duba Lafiyarsa, FG Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kowane shugaba na da damar zaɓan likitocinsa

Da yake zantawa da NAN, Ministan yace shugaban yana da damar zaɓan likitocin da zasu duba lafiyarsa domin ba shine na farko dake fita kasar waje ba.

Muhammed yace:

"A matsayina na ministan labaru yau, idan a baya inada wani likita da na amince da shi, bana tunanin dan nazama minista yanzun zan canza likita na."
"Ba abin damuwa bane kowace kasa likitana yake, ra'ayi na ne in zaɓi likitan da zai duba lafiya ta. Kamar yadda na saba faɗa ba Buhari bane shugaban farko da ya fara fita kasar waje a duba lafiyarsa."
"Idan shugaban ƙasa yana da likitan dake duba lafiyarsa shekaru 30 da suka gabata, wanda yasan abinda ke damunsa, meyasa ya zama wani abu dan ya cigaba da maida hankali ga wannan likitan?"

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Yan Ta'adda Ba Zasu Iya Kwace Najeriya Ba Kamar Afghanistan, Lai

Wane hali ɓangaren kiwon lafiya ke ciki a Najeriya?

Ministan ya nuna damuwarsa ga masu sukar shugaban ƙasa Buhari bisa fita kasar waje a duba lafiyarsa, ya kara da cewa wannan bai kai a soke shi ba, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Muhammed yace duk da kalubalen da Najeriya ke fama da shi, ɓangaren kiwon lafiya bai yi lalacewar da za'a ki amincewa da shi ba.

Ministan ya bayyana cewa duk da sukar da akewa ɓangaren lafiya, amma WHO ta saka Najeriya a matsayi na 4 wajen yaki da cutar COVID19.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Saka Ranar Gangamin Tarukanta Na Kananan Hukumomi

Jam'iyyar APC mai mulki ta sanya ranar 4 ga watan Satumba domin gudanar da gangamin tarukanta na jihohi.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da APC ta fitar ranar Laraba a Abuja ɗauke da sa hannun sakarenta.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

A kwanakin bayane APC ta gudanar da zabukan shugabanninta a matakin gunduma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel