Dalilin da Yasa Wajibi Sheikh Pantami Ya Fito Ya Yi Magana Kan Abinda Taliban Ta Yi a Afghanistan, HURIWA
- Ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam, HURIWA, ta yi kia ga ministan sadarwa, Isa Pantami, yayi tir da Taliban a Afghanistan
- Kungiyar tace ya kamata ministan ya yi amfani da wannan damar wajen tabbatar da baya kan fatawarsa ta baya
- A cewar HURIWA hakan zai sa hankulan yan Najeriya su kwanta game da zargin da akai masa a baya
Abuja - Kungiyar dake fafutukar kare hakkin ɗan adam a Najeriya (HURIWA), ta yi kira ga ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya fito ya yi Allah wadai da kwace mulkin Afghanistan da Taliban ta yi.
A wani jawabi da shugaban HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya fitar ranar Talata, yace yin hakan zai tabbatar da cewa ministan ya canza fatawowin da yayi a baya na tsattsauran ra'ayi.
Jawabin mai taken 'Ya kamata Ministan sadarwa Pantami ya yi Allah wadai da mulkin Taliban a Afghanistan domin nuna ya canza maganganun da yayi a baya.'
Shin dole ne Pantami ya yi magana kan lamarin?
Punch ta ruwaito HURIWA tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya kamata Pantami ya yi tir da Allah wadai da abinda Taliban ta yi a Afghanistan domin ya tabbatar wa duniya cewa baya kan maganganu da fatawowin da aka ruwaito yana yabo kan Taliban da Alqa'ida a baya."
"Muna rokon ministan ya yi amfani da wannan babbar damar da ya samu wajen nesanta kanshi da kungiyar Taliban."
Domin hakan zai zuba ruwan sanyi a zukatan yan Najeriya su yarda cewa ba'a haɗa wata manakisa ta bayan fage da shi akan su."
Shin Pantami ya maida martani?
Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun ministan, Uwa Sulaiman, ba ta ce komai ba game da lamarin.
'Yan Najeriya sun yiwa MKO Abiola addu'a bayan hoton Alkur'ani da ya ba da gudunmawa a wani masallaci ya bayyana
Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyar Taliban ta kwace iko da Kaboul babban birni Afghanistan bayan tsawon shekaru 20 da sojojin Amurka suka fatattake su.
Shugaban ƙasar Afghanistan, Ashraf Ghani, ya fice daga ƙasar tun ranar Lahadi, inda yabar gidan gwamnati ga mayakan Taliban.
A wani labarin kuma Duk Mai Son Gani Bayan IMN Zai Sha Kunya, Sheikh Zakzaky Ya Yi Jawabi Na Farko Bayan Shakar Iskar Yanci
Shugaban kungiyar mabiya akidar shi'a (IMN), Sheikh IbrahIm El-Zakzaky, ranar Talata yace duk mai son wargaza tafiyarsa ba zai ci nasara ba.
Zakzaky yayi wannan maganar ne a taronsa na farko da wakilan kungiyarsa na jihohi da wasu kungiyoyi a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Asali: Legit.ng