Har yanzu bamu kammala bincike kan Abba Kyari ba, Hukumar yan sanda
- Hukumar yan sanda tayi watsi da rahoton cewa an kammala bincike kan Abba Kayri
- A ranar Talata, rahotanni sun nuna cewa kwamitin bincike ta mika sakamakon binciken da tayi ga IGP
- Kakakin hukumar yan sandan Najeriya, CP Frank Mba ya saki jawabin kar ta kwana
Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da cewa binciken da ake gudanarwa kan zargin da Amurka ke yiwa Abba Kyari bai kammalu ba har yanzu, ana cigaba da yi.
Kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya saki jawabin hakan kuma Legit.ng ta samu a ranar Talata, 17 ga Agusta, 2021.
Wani sashen jawabin yace:
"Muna sanar da daukacin jama'a cewa kwamitin bincike bai aika sakamakon bincike ga Sifeto Janar na yan sanda ba, sabanin abinda kafofin yada labarai ke yadawa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan Abba Kyari ya san yana da gaskiya ya mika kansa hannun FBI kawai
Kakakin gamayyar kungiyoyin Arewa CNG, AbdulAzeez Sulaiman, ya bayyana cewa a ra'ayinsa, idan Abba Kyari ya san yana da gaskiya ya mika kansa ga Amurka.
Wannan ya bayyana ne a faifan bidiyon da jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta na Youtube.
AbdulAzeez ya ce wannan ra'ayinsa ce ta kansa saboda bai kamata a rika kare mutum ba tare da wata hujja ba.
A jawabin da yayi, ya ce ya tabbata bai kamata ace Najeriya tace ba za'a bari an kaishi Amurka ba.
Asali: Legit.ng