Karin 'yan Boko Haram sun mika kansu ga sojoji, suna rokon gafaran 'yan Najeriya

Karin 'yan Boko Haram sun mika kansu ga sojoji, suna rokon gafaran 'yan Najeriya

  • Rundunar sojin Najeriya a jihar Borno ta tabbatar da karbar wasu 'yan ta'addan Boko Haram da suka tuba
  • 'Yan ta'addan sun mika wuya ne tare da bayyana nadamar ayyukansu da suka aikata na ta'addanci
  • Hakazalika sun roki 'yan Najeriya da su taimaka su yafe musu, kuma sun yi alkawarin wanzar da zaman laifiya

Maiduguri, Borno - Rahoto daga Daily Trust na shaida cewa, wasu mayakan Boko Haram sun mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.

A cewar majiyoyin soji, ‘yan ta’adda 190 sun mika wuya a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno a ranar Asabar.

An tattaro cewa mazauna garin sun yi mamaki lokacin da suka ga dimbin 'yan ta'addan da suka isa garin Mafa a ranar Asabar.

A cewar majiyar tsaro, wadanda suka mika wuya sun hada da manyan mayaka, sojojin kafa, matansu da yaransu.

Kara karanta wannan

An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara biyu

Karin 'yan Boko Haram sun mika kansu ga sojoji, suna rokon gafaran 'yan Najeriya
Taswirar jihar Borno | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan ta'addan da suka mika wuya sun kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su gafarta musu tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa sun mika wuya cikin son rai, suna masu cewa zaman lafiya ya fi yaki.

Wannan ne karo na farko da 'yan Boko Haram suka mika wuya ga sojoji?

Idan mai karatu zai tuna, sojojin Najeriya sun yi ikirarin cewa jimillar 'yan ta'addan Boko Haram 1081 da iyalansu sun mika wuya ga sojojin a cikin makonni biyu da suka gabata.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan masu tayar da kayar baya da suka mika wuya sun roki 'yan Najeriya da su yafe masu.

Rokon nasu ya haifar da martani iri-iri kamar yadda wasu mutane suka ce ba su cancanci jinkai ba dangane da abubuwan da suka gabata.

Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gurneti ya tashi da kananan yara 5 a Ngala, jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta karba tare da aiwatar da karatun gyaran hali ga 'yan ta'adda da suka mika wuya kafin mika su ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, The Guardian ta ruwaito.

Kakakin rundunar, Brig-Gen. Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne bayan rahotannin da ke cewa rundunar ta yi karatun gyaran hali tare da sakin wasu kwararrun 'yan ta'adda guda biyu masu kirkirar bam.

“An jawo hankalin mu ga rahoton da wasu kafofin watsa labarai na yanar gizo suka buga wanda marubutan da gangan suka jirkita gaskiyar da ke cikin wannan rahoton kuma suka karkatar da shi don dacewa da duk wata manufar da suke son cimmawa.
“Duk da cewa Sojojin Najeriya (NA) ba sa son a raba hankalinsu daga babban abin da suka fi mayar da hankali na magance barazanar da ake yi wa 'yan Najeriya masu son zaman lafiya, ya zama tilas a sanya batutuwan a mahangar da ta dace.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali

"Gaskiya ne cewa a cikin kwanakin baya, sama da membobin Boko Haram 1,000 da danginsu sun mika wuya ga sojoji saboda tsananin matsin lamba daga yawaitar kai farmaki na sojojin.
"Daga cikin wadancan akwai manyan shugabannin kungiyar ta'addancin wadanda suka yi watsi da membobinsu kuma suka mika kansu."

Shugaban hafsun soji ya bukaci jami'ai su yi adalci wajen daukar sabbin sojoji

A wani labarin, Faruk Yahaya, shugaban hafsan sojojin Najeriya, ya yi kira ga hafsoshi da ma’aikatan da ke gudanar da aikin tantance zababbun ma’aikatan rukuni na 81 na shiga aikin sojojin Najeriya da su kasance masu adalci da gaskiya.

Yahaya ya ba da umarnin ne a ranar Asabar, lokacin da ya ziyarci cibiyar horar da sojojin Najeriya da ke sansanin Falgore a jihar Kano, inda ake gudanar da aikin tantancewar.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta a Abuja, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan shirin sakin manyan kwararrun masu hada bama-bamai na Boko Haram

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel