Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali

Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali

  • Rundunar sojin Najeriya ta jaddada cewa, za ta ci gaba da yi wa 'yan ta'adan da suka mika kansu karatun hali
  • Rundunar ta kuma karyata jita-jitan cewa ta saki wasu manyan 'yan ta'adda a watannin da suka gabata
  • Rundunar ta sake jaddada manufar aikinta na samarwa da 'yan Najeriya masu bin doka cikakken tsaro

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta karba tare da aiwatar da karatun gyaran hali ga 'yan ta'adda da suka mika wuya kafin mika su ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa, The Guardian ta ruwaito.

Kakakin rundunar, Brig-Gen. Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne bayan rahotannin da ke cewa rundunar ta yi karatun gyaran hali tare da sakin wasu kwararrun 'yan ta'adda guda biyu masu kirkirar bam.

Sojojin Najeriya za su yi wa tubabbun 'yan ta'adda karatun gyaran hali
Kakakin rundunar sojin Najeriya Hoto: platformsafrica.com
Asali: UGC
“An jawo hankalin mu ga rahoton da wasu kafofin watsa labarai na yanar gizo suka buga wanda marubutan da gangan suka jirkita gaskiyar da ke cikin wannan rahoton kuma suka karkatar da shi don dacewa da duk wata manufar da suke son cimmawa.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan shirin sakin manyan kwararrun masu hada bama-bamai na Boko Haram

“Duk da cewa Sojojin Najeriya (NA) ba sa son a raba hankalinsu daga babban abin da suka fi mayar da hankali na magance barazanar da ake yi wa 'yan Najeriya masu son zaman lafiya, ya zama tilas a sanya batutuwan a mahangar da ta dace.
"Gaskiya ne cewa a cikin kwanakin baya, sama da membobin Boko Haram 1,000 da danginsu sun mika wuya ga sojoji saboda tsananin matsin lamba daga yawaitar kai farmaki na sojojin.
"Daga cikin wadancan akwai manyan shugabannin kungiyar ta'addancin wadanda suka yi watsi da membobinsu kuma suka mika kansu."

A cewarsa, rundunar sojin Najeriya, kasancewar ta kungiyar kwararrun sojoji, za ta ci gaba da yin aiki daidai da abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, da kuma kyawawan ayyuka na duniya.

“Saboda haka, ba daidai ba ne a ce NA za ta saki ' yan ta'adda tubabbu. Don haka, ta yi kira ga jama'a da su yi watsi da karkatar da gaskiyar wadannan kafofin watsa labarai ta yanar gizo kuma su ci gaba da tallafawa NA don kawar da ta'addanci da sauran nau'ikan rashin tsaro."

Kara karanta wannan

Sam ba a yi wa Abba Kyari adalci ba: 'Yan Arewa sun koka kan kwace mukamin Kyari

Saboda jin dadin sojoji, rundunar sojin Najeriya ta samar wa da sojoji jirgin yawo

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa za a samar da jirgin saman zirga-zirga ga sojoji da manyan jami'ai a fagen daga wadanda aka ba izinin ficewa na wucin gadi da nufin zuwa ganin danginsu yayin da suke kan aiki.

Jaridar TheCable ta ba da rahoton cewa izinin ficewar, a yaren sojoji, izini ne na barin sashin aiki na dan wani lokaci.

Legit.ng ta tattaro cewa mafi yawan sojoji da jami'ai da aka tura daga sassa daban-daban na kasar zuwa rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabas suna tafiya daruruwan kilomita lokacin da suke kan izinin ficewa na wucin gadi domin ganin danginsu.

Shugaban hafsun soji ya bukaci jami'ai su yi adalci wajen daukar sabbin sojoji

A wani labarin, Faruk Yahaya, shugaban hafsan sojojin Najeriya, ya yi kira ga hafsoshi da ma’aikatan da ke gudanar da aikin tantance zababbun ma’aikatan rukuni na 81 na shiga aikin sojojin Najeriya da su kasance masu adalci da gaskiya.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu

Yahaya ya ba da umarnin ne a ranar Asabar, lokacin da ya ziyarci cibiyar horar da sojojin Najeriya da ke sansanin Falgore a jihar Kano, inda ake gudanar da aikin tantancewar.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta a Abuja, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel