An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara biyu

An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara biyu

  • Bayan shekara 7, an sake gano daya daga cikin yan matan makarantar Chibok
  • An aurar da ita ga daya daga cikin yan ta'addan Boko Haram kuma har ta haifi yara biyu
  • Sama da yan Boko Haram 100 sun mika wuya kwanan nan

Gwoza, Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya karbi bakuncin daya daga cikin yan matan makarantar Chibok da aka sace tun shekarar 2014 sun zana jarabawar karshe.

Sojojin Najeriya da suka kai matar wajen gwamnan ranar Asabar a garin Gwoza sun ce ita ta mika kanta ga hukuma.

Zulum ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook.

Dalibar mai suna Hassana Adamu, tare da yaranta biyu sun hadu da Gwamna Zulum lokacin da kwamandan 26 taskforce Brigade, Janar DR Dantami, ya kai ta.

Kara karanta wannan

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

Hassana na cikin dalibai mata kimanin 276 da akayi awon gaba da sy daga daga makarantar sakandaren mata dake Chibok, jihar Borno.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara
An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara biyu Hoto: Governor of Borno
Asali: Facebook

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

Shugabannin gargajiya da na addini a Borno sun ce zai yi wahala a sake karbar 'yan Boko Haram da suka tuba cikin garuruwa su.

Shugabannin sun bayyana fargaba kan yadda sojojin Najeriya za su raba tubabbun 'yan Boko Haram da tsattsauran ra'ayi a karkashin shirin su na Safe Corridor.

Abubakar El-Kanemi, Shehun Borno, ya ce wannan abu ne mai kyau, amma mutane za su ci gaba da kasancewa cikin fargaba na bala'in tashin hankalin da aka shafe shekaru 12 ana yi, musamman mazauna garuruwan da za a mayar da masu tayar da kayar bayan.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gurneti ya tashi da kananan yara 5 a Ngala, jihar Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel