Da duminsa: Gurneti ya tashi da kananan yara 5 a Ngala, jihar Borno
- Gurneti ya tashi inda ya fashe da wasu kananan yara biyar kuma suka halaka a karamar hukumar Ngala a Borno
- An gano cewa yaran sun tsinto gurnetin ne yayin da suka fita kiwo a bayan gari kuma suka dinga wasa da shi
- A take yara biyu daga cikin biyar suka sheka lahira yayin da sauran ukun suka rasu a wani asibiti dake Mada a Kamaru
Ngala, Borno - Yara biyar sun halaka yayin da wani gurneti da suke wasa dashi ya fashe a garin Ngala dake jihar Borno, arewa maso gabas na Najeriya kusa da iyakar Kamaru, sojoji suka sanar da AFP a ranar Juma'a.
Yaran kanana uku sun tsinto abu mai fashewan yayin da suka je kiwo a wajen garin kuma ya tashi a hannunsu yayin da suke wasa da shi, cewa Umar Kachalla.
Biyu daga cikinsu sun mutu a take yayin da uku daga cikinsu suka rasu a wani asibiti dake Mada, cikin Kamaru, yace.
Mene ne tushen al'amarin?
Wani mayakin mai suna Umar Ari, ya bada makamancin labarin kan abinda ya faru a ranar Alhamis.
A watan Augustan 2014, mayakan Boko Haram sun kwace Ngala tare da wani birnin kasuwanci mai makwabtaka dasu mai suna Gamboru, Daily Trust ta ruwaito.
Dakarun sojin Najeriya sun kwace biranen biyu a watan Satumban 2015 tare da kokarin dakarun sojin Chadi bayan wata daya da suka kwashe suna yi wa miyagun aman wuta.
Ari ya ce har a yanzu ana samun gurneti daga ragowar wannan arangama tsakanin sojojin da miyagun, hakan yake kawo ajalin yara dake tsintosu.
Daily Trust ta ruwaito yadda a watan Disamban 2019, mutum tara sun halaka kuma 26 suka samu rauni sakamakon abu mai fashewa da ya tashi a gadar data hada Gamboru da Fotokol.
Mazauna yankin sun dora alhakin tashinsa da wani gurnetin da aka gani tamkar abun wasa wanda 'yan ta'addan Boko Haram suka baiwa yara a matsayin kyauta.
Fusatattun Mazauna Kauye sun Sheke Matashin da ya Kashe Abokinsa kan Rikicin Gona
Fusatattun ‘yan kauyen wuraren Sabongida dake garin Iware karkashin karamar hukumar Ardo-Kola a jihar Taraba sun kashe wani mutum wanda ya kashe abokinsa sakamakon cin amana.
Daily Trust ta tattaro bayanai akan yadda wanda ‘yan kauyen suka kashe Jacob wanda yaci amanar abokinsa Mathies Michael, wanda yayi hayarsa don yayi masa aiki a gonarsa ta masara dake kauyensu amma ya lamushe kudin yaki yin aikin.
Asali: Legit.ng