Kyawawan hotuna daga babban taron kungiyar tagwaye na jihar Kano, mutane sun yi martani

Kyawawan hotuna daga babban taron kungiyar tagwaye na jihar Kano, mutane sun yi martani

  • Ƙungiyar Tagwaye ta Jihar Kano ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara kuma kyawawan hotunan membobinta sun haska kafofin sada zumunta
  • A cewar shugaban kungiyar, an kafa gidauniyar domin ta saukaka matsalar tagwaye da ke jihar
  • 'Yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun mayar da martani kan wannan ci gaban

Kungiyar tagwaye ta jihar Kano ta sa mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan sada zumunta bayan gudanar da babban taronta na shekara -shekara.

Da yake magana da BBC Pidgin, shugaban kungiyar da aka bayyana a matsayin Hassan Tijjani Salihu ya ce sun tattauna yadda za a taimaki juna a cikin al'umma.

Kyawawan hotuna daga taron kungiyar tagwaye na jihar Kano, mutane sun yi martani
Kungiyar tagwaye na jihar Kano ta gudanar da babban taronta Hoto: BBC News Pidgin
Asali: Instagram

A cewar Salihu, kungiyar ta kafa wata gidauniya don taimakawa tagwaye da ke da matsala a jihar.

An yada kyawawan hotunan tagwaye a jihar a kafafen sada zumunta kuma 'yan Najeriya sun mayar da martani kan hotunan. Yawancin tagwayen sun yi kama da junansu kuma kowannensu ya sa tufafi iri ɗaya.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame manajar banki shekara 5 kan satar kudin banki N4.8m

Da yake magana game da ƙungiyar, marubucin Najeriya Richard Ali ya rubuta a Facebook:

"Tabbas dole ne ƙungiyar tagwaye ta kasance tana da kwamiti na dindindin kan sasanta rigingimu? Domin mu ‘yan daddaya ba za mu kuskura mu tsoma baki ba a lokacin da Hassana da Hussaina ke musayar zazzafan kalamai ba."

Ga wasu daa cikin martanin jama’a a shafin Instagram:

@maamie_pehbles ta ce:

" 2 2 Allah ya halicci kowa da kowa."

@ominiaho yayi sharhi:

"Menene manufa da hangen wannan ƙungiyar?"

@tams__k ya ce:

"Zan ji wani iri idan zan ga sama da tagwaye 50 a cikin daki. Zan tsorata... idona zai juya.”

@passwordng yayi sharhi:

"Ba da daɗewa ba za su gabatar da buƙatu ga gwamnati."

Matar da aka yi wa gorin rashin haihuwa ta haifi ‘yan uku bayan shekaru da dama

A wani labarin, wata 'yar Najeriya mai suna Hellen Bello ta haifi' yan uku bayan shekaru da dama tana jira.

Kara karanta wannan

Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta

Da ta je shafinta na Facebook don murnar nasarar da ta samu, Hellen ta ce a ƙarshe Allah ya albarkace ta da yara uku a lokaci guda bayan shekaru da yawa ana mata gori.

Asali: Legit.ng

Online view pixel