Matar da aka yi wa gorin rashin haihuwa ta haifi ‘yan uku bayan shekaru da dama

Matar da aka yi wa gorin rashin haihuwa ta haifi ‘yan uku bayan shekaru da dama

  • Bayan shekaru da dama tana jiran haihuwa, wata 'yar Najeriya mai suna Helen Bello ta haifi 'yan uku
  • Matar ta shiga shafukan sada zumunta don murnar nasarar da ta samu sannan kuma ta bayyana cewa an kira ta da sunaye iri a lokacin da bata samu dan kanta ba
  • Ta wallafa kayatattun hotunanta da jariranta kuma nan take 'yan Najeriya suka mamaye sashen sharhi na wallafarta don taya ta murna

Wata 'yar Najeriya mai suna Hellen Bello ta haifi' yan uku bayan shekaru da dama tana jira.

Da ta je shafinta na Facebook don murnar nasarar da ta samu, Hellen ta ce a ƙarshe Allah ya albarkace ta da yara uku a lokaci guda bayan shekaru da yawa ana mata gori.

Matar da aka yi wa gorin rashin haihuwa ta haifi ‘yan uku bayan shekaru da dama
Matar ta dauki tsawon shekaru ba tare da haihuwa ba Hoto: Helen Bello
Asali: Facebook

Sabuwar uwar ta wallafa hotunan lokacin da take da juna biyu da kuma lokacin da jariranta suka iso duniya.

A daya daga cikin hotunan, ana iya ganin Helen a dakin haihuwar tana murmushi yayin da dauki jariranta a kan cinyoyin ta

Kara karanta wannan

An sha ‘yar dirama yayin da amarya ta ki yarda ta sumbaci angonta, jama’a sun yi martani a kan bidiyon

Ta nuna godiya ga Allah da a ƙarshe ya kawo mata agaji kuma ya canza labarin rayuwarta.

'Yan Najeriya sun taya sabuwar uwar murna

Ba da daɗewa ba masu amfani da kafofin sada zumunta suka mamaye sashen sharhi na shafin Helen na Facebook don taya ta murna.

Maimuna Attah ta ce:

"Na yi matukar taya ki murna Allah ya kare ki da 'ya'yanki da sunan Yesu."

Juliana Uche tayi sharhi:

"Ina taya ki murna, Allah Madaukakin Sarki ya albarkaci jariranki Amin."

Batemai Bello Turaki ta rubuta:

"Ina taya ki murna 'yata. Allah ya albarkace su kuma ya kiyaye su, ina miki fatan samun lafiya da ƙarfi."

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’ 100 da shan madara lita 6 a kullun

A wani labarin, wata mata 'yar kasar Mali da ta haifi yara tara a lokaci guda a ranar 5 ga watan Mayu, 2021, a kasar Maroko, ta bayyana cewa yaran suna amfani da ‘pampers’guda 100 a rana guda.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Kutsa Wurin Ibada Sun Hallaka Babban Malami Yana Tsaka da Addu'a

Halima Cisse, wacce ta haifi yaran a cikin asibitin Casablanca, ta shaida wa Daily Mail cewa jariran na shan lita shida na madara a kowace rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng