Kotu ta garkame manajar banki shekara 5 kan satar kudin banki N4.8m

Kotu ta garkame manajar banki shekara 5 kan satar kudin banki N4.8m

  • Manajar banki zata kwashe shekaru biyar a magarkama kan laifin satan kudi a wajen aiki
  • Ta amsa dukkan laifukan da aka zargeta da su a kotu
  • Bayan hakan kotu ta umurceta ta mayar da kudin da ta sace

Kotu ta bada umurnin jefa wata manajar banki gidan gyaran hali na tsawon shekaru biyar kan laifin rashawa da alnundahana a jihar Bauchi, Arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan ya biyo bayan shigar da ita kotu da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC tayi .

Sarita Aliyu ta kasance Dirakta Manajar bankin Workman Microfinance Bank lokacin da ta wawure N4.8 million daga cikin asusun bankin.

EFCC tace matar ta yi amfani da lambar sirrin shugaban sashen kudi wajen rubuta sunayen wasu mutanen bogi don bukatar bashi.

Hukumar ta bayyana hakan a jawabin da ta saki a shafinta na Facebook ranar Laraba.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke yaro da mahaifiyarsa wacce ya tsoma a harkar damfara ta yanar gizo

Kotu ta garkame manajar banki shekara 5 a kurkuku
Kotu ta garkame manajar banki shekara 5 kan satar kudin banki N4.8m Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Bisa binciken da EFCC tayi, ta amince da wadannan basussukan na bogi kuma ta biya kanta kudi N4,786,700.

EFCC ta bayyanawa babbar kotun Bauchi cewa Sarita Aliyu ta saba dokoki na sashen 308, 363 na Penal Code.

Sarita Aliyu ta amince da zargin da ake mata kuma Alkalin MM Abubakar ta yanke mata hukuncin shekaru biyar a gidan gyaran hali.

Bayan haka, kotu ta umurceta da ta biya bankin kudi N3.8 million.

EFCC ta cafke yaro da mahaifiyarsa wacce ya tsoma a harkar damfara ta yanar gizo

A wani labarin kuwa, Hukumar EFCC a shiyyar Kaduna ta cafke wasu mutane hudu da suka hada da Lucky Ebhogie, Richman Kas Godwin, Israel Justin da Precious Iwuji da aikata laifin zambar ta yanar gizo.

An damke su ne a ranar 5 ga Agusta, 2021, a unguwar Sabo da ke Kaduna, a Jihar Kaduna biyo bayan bayanan sirri kan zarginsu da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Ranar kin dillaci: EFCC ta karbe manyan gidaje, motoci da miliyoyi a hannun wasu ‘Yan damfara 2

Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin galibi suna da hannu cikin aikata zamba da kulla soyayyar karya soyayya; yin karya da sunan ma'aikatan sojin Amurka akan ayyukan kasashen waje don yaudarar mutanen da suka fada fatsarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel