Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta

Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta

  • Hasashen masana na kara tabbatarwa cewa, Osinbajo ne ya fi cancanta da gadon kujerar Buhari
  • Wannan na zuwa ne daga wata kuri'a da jaridar ThisDay ta gudanar kan shugaban da ya fi cancanta
  • Masana sun bayyana nagartar Osinbajo ta fuskoki da dama wanda suke ganin shi ne mafi cancanta

Abuja - Yayin da ake tattaunawa game da wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba a 2023, masana sun bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin dan takarar da yafi nagarta, kamar yadda yazo a kuri'ar da jaridar ThisDay ta yi.

Kuri'ar ya biyo bayan hirar da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida yayi da gidan talabijin na Arise TV akan wanda zai zama shugaban Najeriya a 2023.

Ra'ayoyin al'umma kan tsayawar Osinbajo ya takarar shugaban kasa na karuwa
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Osinbajo shi ya cancanci zama shugaban kasa

Baya ga cancantar ilimi, Babangida ya ambaci shekaru da gogewa a matsayin muhimman abubuwan da za su sa a zabi wanda zai maye gurbin Buhari a 2023, inda ya bayyana a sarari cewa ya kamata 'yan Najeriya su zabi mutum mai kuzari wanda bai haura shekaru 60 ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: An ambaci sunan Osibanjo a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari

Kuri'ar da jaridar ta wallafa a ranar Litinin ta kawo wasu fitattun 'yan Najeriya, tare da Osinbajo cikinsu a matsayin wadanda suka cancanta su rike manyan mukamai a nan gaba.

Sauran wadanda aka kawo sun hada da Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka, Dakta Akinwunmi Adesina da Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Misis Amina Mohammed.

Hakazalika da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, da gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, da sauransu.

Gina sharhin su kan sharuddan da tsohon shugaban na soji Babangida, su ne: tsohon shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, Dakta Sam Amadi, ya ce Osinbajo ya fi cancanta fiye da sauran dukkan mutane 30 da aka lissafa a cikin rahoton ThisDay.

Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

A wani labarin, Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri'ar amincewa da kwamitin rikon kwarya wanda takwaransu gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yake jagoranta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

Gwamnonin sun bayyana cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaɓen gwamnan jihar Ondo ya nuna cewa kwamitin na kan doka.

Gwamnonin sun yi wanna jawabin ne a taron da suka gudanar ranar Litinin domin tattauna matsalolin da suka taso a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel