Zargin almundahana: Jerin tsoffin gwamnoni 4 da EFCC ta bincika kwanan nan

Zargin almundahana: Jerin tsoffin gwamnoni 4 da EFCC ta bincika kwanan nan

A makwannin da suka gabata, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gayyaci wasu fitattun tsoffin gwamnoni domin yi musu tambayoyi yayin da take kokarin karfafa yaki da cin hanci da rashawa.

Rahotannin kafofin watsa labarai sun nuna cewa an yi wa tsoffin gwamnonin tambayoyi dangane da zarge -zargen cin hanci da rashawa daban-daban da ake zarginsu da hannu a ciki lokacin da suke kan mulki.

Zargin almundahana: Jerin tsoffin gwamnoni 4 da EFCC ta bincika kwanan nan
EFCC ta binciki wasu tsoffin gwamnoni kan zargin rashawa Hoto: Abubakar Bukola Saraki, Henry Seriake Dickson, Alh Umaru Tanko Almakura, Governor Rochas Okorocha
Asali: Facebook

Ga tsoffin gwamnonin da hukumar yaki da rashawar ta bincika a kwanan nan:

1. Bukola Saraki

A kwanan nan ne aka yi wa Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya, tambayoyi kan sabon zargin sata da handame kudade.

Saraki wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Kwara ya kasance a ofishin EFCC a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli.

An tattaro cewa an yi masa tambayoyi game da zargin sata da wawure kudaden gwamnati ta hanyar amfani da kamfanonin karya.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta yi wa tsohon Gwamna da wasu mambobin APC 5 tambayoyi kan taron kin jinin Buhari

2. Tanko Al-Makura

A ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci, Tanko Al-Makura, da matarsa, Mairo, sun amsa tambayoyi daga EFCC a ofishin hukumar.

Rahotanni sun ce an yi wa Al-Makura tambayoyi kan zargin cin amana da almubazzaranci da kudade a lokacin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

Al-Makura ya yi gwamnan jihar Nasarawa tsakanin 2011 zuwa 2019 kafin a zabe shi a majalisar dattawa don wakiltar yankin Nasarawa ta Kudu.

3. Seriake Dickson

Jami'an EFCC sun sanya wa tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Seriake Dickson zafi a ranar Talata, 10 ga watan Agusta.

Hukumar ta yi masa tambayoyi bayan ya gabatar da kansa sakamakon gayyatar da aka yi masa a baya-bayan nan.

An tattaro cewa an yi ma Dickson wanda a halin yanzu yake wakiltar Bayelsa ta yamma a majalisar dattijai tambayoyi kan zarge-zargen cin mutuncin kujerar mulki da karkatar da dukiyar gwamnati a lokacin mulkinsa na shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta titsiye tsohon gwamna a Najeriya, tana tuhumarsa

4. Rochas Okorocha

Hukumar EFCC ta rahoto cewa ta damke tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, a ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, a ofishinsa na Unity House da ke Abuja.

An ce an damke dan siyasar ne bayan kai ruwa rana na sa’o’i biyar da suka yi da jami’an EFCC da suka bi shi zuwa wurin.

Hakan ya biyo bayan kin amsa gayyata da dama daga hukumar lamarin da ya sa hukumar ta tura jami'anta domin su bibiye shi.

An yi masa tambayoyi a kan zargin almundahana da aka yi a lokacin da ya yi gwamna na shekaru takwas.

Okorocha ya shafe kwanaki biyu a hannun hukumar EFCC kafin a sake shi.

Hukumar DSS ta yi wa tsohon Gwamna da wasu mambobin APC 5 tambayoyi kan taron kin jinin Buhari

A wani labari na daban, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa Jibrilla Bindow, tsohon gwamnan jihar Adamawa tambayoyi a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

FG na bibiyar Kanu da Igboho amma ta kyale barayin makiyaya, Gwamnan Arewa

Sadiq Abdullateef, hadimin tsohon gwamnan, ya shaidawa jaridar cewa Bindow ya amsa gayyatar hukumar DSS kuma an sake shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel