Hukumar DSS ta yi wa tsohon Gwamna da wasu mambobin APC 5 tambayoyi kan taron kin jinin Buhari

Hukumar DSS ta yi wa tsohon Gwamna da wasu mambobin APC 5 tambayoyi kan taron kin jinin Buhari

  • Rundunar 'yan sandan farin kaya ta Najeriya, DSS, ta yi wa tsohon gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow tambayoyi kan halartar taron batanci ga Buhari
  • An ce Bindow ya kasance a wurin wani taro inda wasu 'yan jam'iyyar APC suka yi mugun fata ga Shugaba Buhari
  • DSS ta kuma yi wa wasu mambobin APC biyar da suka halarci taron tambayoyi

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa Jibrilla Bindow, tsohon gwamnan jihar Adamawa tambayoyi a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, jaridar TheCable ta ruwaito.

Sadiq Abdullateef, hadimin tsohon gwamnan, ya shaidawa jaridar cewa Bindow ya amsa gayyatar hukumar DSS kuma an sake shi.

A cewar jaridar, 'yan sandan sirri sun yi hira da Bindow tare da wasu mutane biyar, da suka hada da:

1. Kabiru Mijinyawa, tsohon kakakin majalisar dokokin Adamawa

2. Sulaiman Adamu, shugaban riko na jam’iyyar APC Yola ta kudu

Kara karanta wannan

Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar Hamayya YPP

3. Mustapha Barkindo, tsohon mai ba da shawara a lokacin gwamnatin Bindow

4. Abubakar Umar Sirimbai, tsohon kwamishina

5. Yusha’u Adamu

Hukumar DSS ta yi wa tsohon Gwamna da wasu mambobin APC 5 tambayoyi kan taron kin jinin Buhari
Hukumar DSS ta yi wa Bindow tambayoyi Hoto: News from the GOVT. HOUSE YOLA Office Of The S.A Press & Media Affairs
Asali: Facebook

An tattaro cewa tsohon gwamnan ya yi wani taron jam'iyya a Adamawa inda wasu fusatattun mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka yi batanci ga Shugaba Muhammadu Buhari.

An fitar da wan faifan ganawar ga manema labarai, kuma an ce wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun yi fatan mutuwa ga shugaban kasar.

Hukumar DSS ta gayyaci manyan mahalarta taron don yi masu tambayoyi a kan faifan sauti da aka fallasa.

Bindow ya yi Allah wadai da masu kalaman batancin kan Buhari

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Abdullateef ya ce tsohon gwamnan ya yi Allah wadai da masu kalaman batanci ga shugaban kasar a taron.

Sanarwar ta ce:

"An gayyaci tsohon gwamnan jihar Adamawa, Sanata Muhammad Umar Jibrilla Bindow zuwa taron jam'iyyar saboda wasu mambobin jam'iyyar sun fusata game da zaben fidda gwani da aka kammala, wanda ya halarta a matsayin dattijon jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Da so samu ne, da Korona ta kashe Buhari mun huta: Shugaban APC a Yola

“Ya cancanci a lura cewa, babu wani shiri a cikin taron da aka ce, ya je can ya zauna ya saurari korafe -korafen mambobin, kuma akwai furuci da ba daidai ba daga wasu membobi wanda ya yi gargadi, abin bakin ciki ne cewa wasu mutane suna amfani da wanda ya harzuka tare da nadir murya don cin mutuncin tsohon gwamnan.
“Shiri ne wannan muryar da aka nada kuma idan kun saurare shi sosai, akwai wasu maganganun da aka tsallake, Sanata Bindow ya gargadi membobin da ke yin waɗannan maganganun marasa inganci sau uku a cikin taron har ma da barazanar ficewa.
“Kalamansa sun kasance, 'Don Allah wannan bai dace ba, ba a yi wa wani fatan mutuwa saboda dalilai na siyasa, ku takaita magana game da shugabanmu kuma uba, shugaban kasa. Ku bari mu ci gaba don Allah, ko na tafi '.
"Amma saboda an shirya abun don yin ɓatanci da haifar da matsaloli ainda babu ne, maganganunsa na yin Allah wadai da abin da aka faɗi ba ma ya cikin faifan da aka watsa.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP

"Shugaba Muhammadu Buhari tamkar uba ne ga Bindow kuma ba zai taba jin dadin irin wannan a kan shugaban kasar ba."

SWC ta dakatar da Shugaban APC mai yi wa Buhari fatan ya mutu, Osinbajo ya hau mulki

A baya mun kawo cewa jam’iyyar APC ta dakatar da shugabanta na rikon kwarya na karamar hukumar Yola ta kudu, jihar Adamawa, Alhaji Sulaiman Adamu.

Gidan talabijin na TVC ya kawo rahoto a ranar Talata, 10 ga watan Agusta, 2021, cewa an dauki matakin nan ne saboda zargin Sulaiman Adamu da ake yi da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel