FG na bibiyar Kanu da Igboho amma ta kyale barayin makiyaya, Gwamnan Arewa

FG na bibiyar Kanu da Igboho amma ta kyale barayin makiyaya, Gwamnan Arewa

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya sake caccakar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari
  • Ortom ya ce gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen bibiyar masu fafutukar neman ballewa yayin da ta kyale barayin makiyaya suna cin karensu ba babbaka
  • Ya kalubalanci gwamnati da ta yi amfani da irin karfin da ta yi amfani dashi kan Igboho da Nnamdi Kanu wajen magance matsalar rashin tsaro

Makurdi, Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya sake caccakar gwamnatin tarayya saboda rashin jajircewa wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

A cewar gwamnan, jami'an tsaro a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun nuna karfinsu ta hanyar cafke jagoran 'yan asalin yankin Biafra, Nnamdi Kanu; da mai fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo wato Sunday Igboho.

Ortom, wanda ya yi magana a shirin ‘NewsNight’ na Channels Television a ranar Litinin, ya kalubalanci gwamnatin Buhari da ta bi bayan ‘yan bindiga da makiyayan da ke kisa, yi wa mata fyade da yin garkuwa da mutane a duk fadin kasar kamar yadda ta yi wajen bin ‘yan aware.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

FG na bibiyar Kanu da Igboho amma ta kyale barayin makiyaya, Gwamnan Arewa
Gwamna Ortom ya kalubalanci gwamnatin tarayya da ta magance matsalar tsaro Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa a cikin 'yan watannin da suka gabata, fafutukar masu neman ballewa, wanda Kanu da Igboho ke jagoranta ya yi zafi a yankin Kudancin kasar.

Masu fafutukar sun ambaci rashin adalci wajen rabon albarkatu da nadin mukamai a ofisoshi masu mahimmanci, rashin tsaro, rashin ci gaba, daga cikin dalilansu na son barin ƙasar.

DSS na tsare da Kanu wanda aka kamo daga kasar waje kuma yana fuskantar tuhuma ta ta’addanci a gaban Justis Binta Nyako a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A gefe guda kuma, an damke Igboho a filin jirgin sama da ke Jamhuriyar Benin yayin da yake kokarin hawa jirgi zuwa kasar Jamus.

Mai fafutukar ya shafe kimanin makwanni uku a wani gidan yarin Benin yayin da Gwamnatin Najeriya ke kokarin ganin an mika shi gare ta.

'Yan Najeriya da dama na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan gwamnatin Buhari kan zargin kyale 'yan ta'adda da ke kai hare-hare a yankin arewacin kasar yayin da jami'an tsaro ke bi ta kan Igboho, Kanu da sauran ‘yan aware.

Kara karanta wannan

A yanzu kam manufar mu ita ce sama wa 'yan Najeriya aiki, in ji Gwamnatin Buhari

Da yake magana a daren Litinin a matsayin bako a cikin shirin talabijin wanda The Punch ta bibiya, Ortom ya yi zargin cewa Fulani makiyaya na ci gaba da kai wa jiharsa hari saboda ya hana kiwo a fili.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

“Na ji an kama Sunday Igboho. Da irin wannan jajircewar, yana nuna cewa Gwamnatin Tarayya tana da karfin iko."

Ortom ya ce sama da mutane miliyan daya da rabi ne suka rasa muhallansu a jihar Benue sakamakon hare -haren da maharan suka kai, ya kara da cewa gwamnatin All Progressives Congress ta gaza a dukkan fannonin gudanar da mulki.

Ka Ƙyalle Buhari Ya Wataya: Ƙungiyar Tibi Ta Faɗa Wa Gwamnan Benue Samuel Ortom

A wani labarin, kungiyar Matasan Tibi ta yi kira ga Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya mayar da hankali kan samar da mulki na gari ga mutanen jiharsa a maimakon bata lokaci da sunan sukar Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Kungiyar ta Tiv Youth Council Worldwide ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugabanta, Hon Mike Msuaan ya fitar.

Daily Trust ta ruwaito Musuaan ya ce bai san dalilin da yasa gwamnan ke gaggawar neman abin da zai hada shi da shugaban kasa ba don jaridu su dauka a yayin da akwai ayyuka da dama na gwamnati da ke bukatar kulawansa a jiharsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng