Da duminsa: EFCC ta titsiye tsohon gwamna a Najeriya, tana tuhumarsa
- Rahotonni sun bayyana yadda EFCC suka titsiye tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Seriake Dickson a ranar Talata 10 ga watan Augusta
- Jami’an hukumar sun gayyaceshi ne don ya amsa tambayoyi bisa zargin wawurar kudade da kadarorin gwamnatin jihar Bayelsa
- Tsohon gwamnan ya isa hedkwarar EFCC dake Jabi a Abuja da misalin karfe 11am don ya warware zare da abawa akan zargin da ake masa
FCT, Abuja - Rahotonni sun bayyana akan yadda jami’an EFCC suka hadawa tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson, zafi a ranar Talata, 10 ga watan Augusta.
Seriake ya sha tambayoyin kurar hali a gaban jami’an bayan ya bayyana a gaban jami’an bayan sun gayyaceshi.
EFCC tana zargin Dickson da rubda ciki kan kudin jihar yayin da yake mulki
An tattara bayanai akan yadda gwamnan mai wakiltar Bayelsa na yamma ya sha tambayoyi akan yadda ya tozarta ofishinsa ta hanyar wadaka da dukiyar al’umma na tsawon shekaru 8 da yayi mulki.
Wata majiya wacce tayi magana da The Nation akan lamarin ta ce:
Tsohon gwamnan ya bayyana a hedkwatar EFCC dake Jabi dake Abuja da misalin karfe 11am ya sha tambayoyi a gaban jami’an bisa zargin wawurar dukiyar al’umma.
Sai dai babu bayanai daki-daki akan abubuwan da ake zargin gwamnan dashi a halin yanzu, zargin sun hada da wulakanta matsayinsa ta hanyar almundahana da wawurar dukiyar al’umma.
An samu labarin gayyatar da EFCC suka yi wa tsohon gwamnan kudu kudu daga shugaban yada labaran hukumar.
Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami
Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami SAN, ya musanta rahotanni dake yawo na cewa ya bijirewa umarnin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kan zabukan jam'iyyar APC.
Daga cikin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Osinbajo yayi taron manyan lauyoyi na jam'iyyar a ranar 30 ga watan Yuli domin shawo kan matsalar dake cikin jam'iyyar bayan kotun koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnoni na jihar Ondo.
Akwai rahotanni dake yawo na cewa Osinbjo ya umarci Malami da kada a yi zabukan jam'iyyar na jihohi, Daily Trust ta wallafa.
Asali: Legit.ng