Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

  • Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri'ar amincewa da jagorancin kwamitin riko na Buni
  • Gwamnonin sun ce hukuncin kotun koli na zaɓen gwamnan Ondo ya kara tabbatar da cewa kwamitin na kan tsarin doka
  • Hakanan sun ce kwamitin da takwaransu Mai Mala Buni yake jagoranta yana aiki mai kyau wajen shirya APC gabanin zaɓen 2023

FCT Abuja - Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri'ar amincewa da kwamitin rikon kwarya wanda takwaransu gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yake jagoranta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnonin sun bayyana cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaɓen gwamnan jihar Ondo ya nuna cewa kwamitin na kan doka.

Gwamnonin sun yi wanna jawabin ne a taron da suka gudanar ranar Litinin domin tattauna matsalolin da suka taso a jam'iyyar.

Shugaban kwamitin riko, Gwamna Mai Mala Buni
Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Taron wanda ya gudana a gidan gwamnan Kebbi dake Asokoro, ya samu jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Atiku Ya Magantu Kan Rikicin Dake Faruwa a Jam'iyyar PDP, Ya Fadi Mafita

Kwamitin rikon kwarya ya sha yabo

Gwamna Atiku Bagudu yace kwamitin rikon kwarya bisa jagorancin Mai Mala Buni ya yi namijin kokari wajen saita jam'iyyar ta APC

A jawabinsa yace:

"Kwamitin rikon kwarya bisa jagorancin Buni ya yi aiki mai kyau wajen saita APC da kuma kara wa jam'iyyar karfi da shiri yayin da zaɓen 2023 ke kara gabatowa."

Taron ya kara jaddada cewa amincewar gwamnonin APC zai kara wa jam'iyyar karfin guiwa wajen cigaba da garambawul ɗin da take yi.

Hakanan zai taimaka wajen saita jam'iyyar ta hanyar ƙara mata karfi yayin da ake cigaba da tarukan APC a faɗin kasa.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Jam'iyyar APC a jihar Neja

Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, a yankin karamar hukumar Mariga, jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Bobi ne yayin da ya je gonarsa domin sanya ido ga masu masa aiki ranar Asabar da yamma.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Majalisa Sun Zabtare Kudaden da Tsaofaffin Gwamnoni Suke Karba Duk Wata

Asali: Legit.ng

Online view pixel