Shugabancin 2023: An ambaci sunan Osibanjo a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari

Shugabancin 2023: An ambaci sunan Osibanjo a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari

  • Kungiyar Osinbajo Grassroots Organisation ta yaba da wasu halayen jagoranci na mataimakin shugaban Najeriya, Osinbajo
  • Kungiyar goyon bayan ta ce yana da matukar muhimmanci 'yan Najeriya su zabi shugaban da zai iya ciyar da kasa gaba
  • A cewar shugaban kungiyar na kasa, Foluso Ojo, iya jagoranci Yemi Osinbanjo a bayyane suke

FCT, Abuja - An ambaci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin wanda ya fi dacewa ya gaji shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Wata kungiya mai suna Osinbajo Grassroots Organisation (OGO) ta bayyana mataimakin shugaban kasa a matsayin hanya madaidaiciya ga makomar Najeriya daga 2023, inji rahoton The Cable.

Shugabancin 2023: An ambaci sunan Osibanjo a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari
Kungiyar ta ce Osinbajo ne ya cancanci ya gaji Shugaba Buhari Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar na kasa, Foluso Ojo, a cikin wata sanarwa a Abuja, ya bayyana cewa kungiyar ta ware 8 ga watan Agusta don gudanar da taron murna na Osinbajo.

Ya ce kwarewar jagoranci na mataimakin shugaban kasa na nuna cewa zai iya maye gurbin Buhari a 2023 kuma ya ci gaba kan abin da ta bayyana a matsayin kyakkyawan shiri na gwamnatin mai ci.

Kungiyar ta ce:

“Mun gano a tattare da mataimakin shugaban kasa halin jagoranci mai cike da nagarta; mutum wanda zai iya ci gaba da ayyukan alherin da Shugaba Muhammadu Buhari ya riga ya fara."

Kungiyar ta OGO ta bayar da hujjar cewa Osinbajo yana da cancanta, halayya, da sha’awar ciyar da kasa gaba, The News ta ruwaito.

Kungiyar ta bayyana cewa taron yana nufin gamsar da mataimakin shugaban kasa ya yarda da tsayawa takarar shugaban kasa.

A cewar jagoran kungiyar, taron zai gudana ne ta yanar gizo da kuma ido da ido a Abuja da jihohi a fadin tarayya da kuma bin ka’idojin COVID-19.

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja IBB ya yi waje da Atiku, Tinubu daga zaben 2023

A wani labarin, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata 'yan Najeriya su zabi tsofaffin 'yan siyasa ba a 2023.

Babangida, wanda ake kira IBB, ya fada a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta, cewa kasar na bukatar wani matashi mai kwazo da zai karbi mulki daga hannun Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel