Shugaba Buhari Ya Cika Dukkan Alkawarin da Ya Yi Wa Yan Najeriya Kafin a Zabe Shi, Jigo

Shugaba Buhari Ya Cika Dukkan Alkawarin da Ya Yi Wa Yan Najeriya Kafin a Zabe Shi, Jigo

  • Wani jigon jam'iyya mai mulki ya yi ikirarin cewa shugaba Buhari ya cika alkawurran da ya ɗaukar wa yan Najeriya
  • Terhemba Ishegh, yace duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fama da shi, Buhari ya aiwatar da ayyuka
  • Ya ƙara da cewa Buhari ya yi abinda babu wani shugaban ƙasa da ya iya aiwatarwa a shekara shida

Jigon jam'iyyar APC a jihar Benuwai, Terhemba Ishegh, yace shugaba Buhari ya cika mafi yawan alƙawurran da ya ɗauka yayin yakin neman zaɓensa ga yan Najeriya, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Mr. Ishegh, wanda tsohon sakataren dindindin ne a jihar Benuwai, ya faɗi hakane yayin wata fira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a makurɗi.

Yace Buhari ya kafa ayyuka da dama duk da ƙalubalen tsaron da ƙasar nan ke fama da shi, amma duk da haka gwamnatinsa ba ta yi ƙasa a guiwa ba har sai da ta cimma nasarori da dama.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki, Ta Fadi Dalili

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari Ya Cika Dukkan Alkawarin da Ya Yi Wa Yan Najeriya Kafin a Zabe Shi, Jigo Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewarsa, gwamnatin Buhari ta samu nasarori da dama a ɓangaren kayayyakin gwamnati, ilimi, tattalin arziki da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Buhari ya kafa tarihi

Ishegh ya ƙara da cewa duk da halin kakanikayi da kasar nan ta faɗa, gwamnatin Buhari tayi kokari wajen aiwatar da manyan ayyuka a faɗin Najeriya.

Yace: "Buhari ya yi namijin kokari a mafi yawan yankuna, wasu yankunan ya fara zuba musu ayyuka amma sai wasu matsaloli su hana karisawa."

"A jimulla zan iya cewa shugaba Buhari ya kafa tarihin da babu wani shugaban Najeriya da ya taba yi a cikin shekaru shida."

"A halin yanzu, duk da ƙalubalen tsaron da ake fama da shi kala daban-daban a yankunan Arewa-yamma, arewa-gabas, da arewa ta tsakiya sannan ya matsa zuwa kudu-yamma kudu-gabas."

"Amma gwamnati bata yi ƙasa a guiwa ba ta cigaba da yin iyakar kokarinta wajen kawo karshen matsalar a waɗannan yankuna," inji shi.

Kara karanta wannan

Ku Mun Adalci Wajen Rubuta Nasarori Na, Shugaba Buhari Ga Marubuta Tarihi

Yan Najeriya suna walwalawa

Mr. Ishegh, yace idan ma aka cire shirye-shiryen da gwamnati ta kirkiro na walwala da jin daɗi ga talakawan Najeriya, Buhari ya samu damar aiwatar da muhimman ayyuka a kowane sashin ƙasar nan.

Ya bayyana irin waɗannan muhimman ayyuka da suka hada da hanyoyi, gada, makarantu da kuma garambawul ga ɓangaren samar da hasken wutar lantarki domin haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa.

A wani labarin kuma Manyan Masu Fada Aji Na Arewa Ke da Alhakin Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Matawalle Ya Fallasa

Gwamnan jihar Zamfara , Bello Matawalle, a ranar Lahadi, yace shugabannin arewa ke da alhakin matsalar tsaron da ya mamaye yankin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Yace shugabannin arewa suke da alhakin yanayin da yankin ke ciki, wanda ya haɗa da aikata manyan laifuka kamar fyaɗe, kisan mata da ƙananan yara, sace mutane, fashi da makami da sauran manyan laifukan da suka mamaye yankin.

Kara karanta wannan

Bangaren Ilimi Muka Fi Baiwa Muhimmanci a Gwamnati, Shugaba Buhari Ya Sake Yin Alkawari

Asali: Legit.ng

Online view pixel