Ku Mun Adalci Wajen Rubuta Nasarori Na, Shugaba Buhari Ga Marubuta Tarihi
- Shugaban ƙasa Buhari ya yi kira ga marubuta tarihi a Najeriya da su yi wa gwamnatinsa adalci
- Shugaban yace gwamnatinsa ta fuskanci ƙalubale da dama tun lokacin da ta zo a shekarar 2015
- Buhari ya bayyana cewa farashin man fetur ya faɗi warwas a karkashin gwamnatin sa
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga masana tarihi da masu hankali cewa su yi wa gwamnatinsa adalci wajen rubuta nasarorin da ta samu, kamar yadda the cable ta ruwaito.
A wani jawabi da Malam Garba Shehu ya fitar, Kakakin shugaban ƙasa, Buhari ya yi wannan kira ne yayin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin APC a mahaifarsa, Daura, jihar Katsina.
Buhari yace: "Mutane masu hankali da kuma marubuta tarihi ya kamata su yi adalci akan mu. Waɗanda suke neman wani muƙami ba zasu gurbata abinda mutane suka gani a ƙasa ba."
Mun yi namijin kokari
Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi namijin kokari wajen ceto ƙasar nan idan aka kwatanta da yanda ƙasar take a 2015.
Yace: "Cigaban da aka samu a yankin arewa maso gabas abin jin dadi ne, domin a wancan lokacin mutanen dake rayuwa tare, suke magana da yare iri ɗaya, sune suka fara kashe junansu."
"Idan kuka duba yanayin da gwamnatin mu ta tsinci ƙasar nan ta ɓangaren lokaci da kuɗaɗen shiga, zaku fahimci abubuwan da muka cimma wa."
Legit Hausa ta tuntubi wata masaniya tarihi, Aisha Musa, wacce ta bayyana ra'ayinta kan maganar shugaba Muhammadu Buhari.
Aisha Musa tace ya kamata shugaba Buhari ya sani cewa masana tarihi abin da ya faru suke katabtawa, na alkhairi da na sharri kuma ba abinda mutum ke so ba.
Tace:
"A matsayinmu na masana tarihi, muna aiki ne da hujjoji, ba kawai rubutu muke yi ba, muna bincike sannan mu fassara muyi sharhi."
"Saboda haka ka saurari ganin komai (na alkhairi da na sharri) ba abinda zai maka dadi kawai ba."
Farashin gangar mai ya faɗi
Buhari ya ƙara da cewa daga zuwan gwamnatinsa farashin man fetur ya yi warwas a kasuwar duniya daga sama da dala $100 ya koma ƙasa da $38.
Hakanan a wancan lokaci ana haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 2.1m a rana ɗaya amma ya dauka zuwa ganga 500,000.
"Mun yi iyakacin kokarin mu, kuma mun gode Allah mun samu nasarori da dama, in banda haka da yanzun mun shiga matsala," inji Buhari.
Asali: Legit.ng
Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng
Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262