Bangaren Ilimi Muka Fi Baiwa Muhimmanci a Gwamnati, Shugaba Buhari Ya Sake Yin Alkawari

Bangaren Ilimi Muka Fi Baiwa Muhimmanci a Gwamnati, Shugaba Buhari Ya Sake Yin Alkawari

  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa zata cigaba da baiwa ilimi muhimmanci sosai
  • Shugaban ya faɗi hakane a Daura, yayin da ya karbi baƙuncin malamai da ɗaliban wata makaranta mai zaman kanta a Daura
  • Shugaban ya sha alwashin kara wa ɓangaren ilimi kasafin kuɗi domin ƙara inganta koyo da koyarwa

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa inganta ilimi a ƙasar nan zai cigaba da kasancewa a sahun gaba wajen abubuwan da gwamnati zata fi baiwa muhimmanci, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tashin Hankali Yayin da Wasu Yan Bindiga Suka Hallaka Manoma 5 a Jihar Nasarawa

Shugaban ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin ɗalibai da shugaban makarantar Premier Pacesetters a gidansa dake Daura, jihar Katsina ranar Alhamis, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaba Buhari tare da dalibai a Daura
Bangaren Ilimi Muka Fi Baiwa Muhimmanci a Gwamnati, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau FB Fage
Asali: Facebook

A wani jawabi da kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya fitar ɗauke da sanya hannunsa, yace:

"Shugaba Buhari ya ƙara tabbatar da za'a ƙara himma sosai domin samar da cigaba a ɓangaren ilimi."

Malam Shehu ya hakaito shugaba Buhari na cewa: "Zamu ƙara yawan kuɗaɗe a ɓangaren ilimi don samar da cigaba a koyo da koyarwa a kokarin mu na farfado da ɓangaren ilimi a Najeriya."

Dabi'a na da muhimmanci a koyon ilimi

A cikin jawabin Malam Garba Shehu, yace: "Buhari, wanda ya ɗauki lokaci tare da ɗalibai ƙananan yara, ya jaddada muhimmancin ɗabi'a mai kyau a wajen neman ilimi, ya kuma roƙe su kada su gaza a karatunsu."

"Malamar makarantar, Mrs. Celine Friday, ta isar da sakon barka da sallah ga shugaban a madadin malamai da ɗaliban makarantar baki ɗaya kuma ta yaba wa gwamnatinsa bisa kulawa ta musamman da take baiwa ilimi."

KARANTA ANAN: Zan Jingine Siyasa a 2023 Domin In Koma Aikin Tallafawa Mutane, Gwamnan Arewa

"Ta kuma yi amfani da wannan damar wajen mika kokon bara ga gwamnatin tarayya da ta taimakawa makarantu masu zaman kansu musamman na yankunan karkara."

A wani labarin kuma Maganar da Sarkin Muri Ya Yi Ranar Sallah Kan Fulani Makiyaya Ta Bar Baya da Kura

A ranar Talata, ranar da al'ummar musulmi suka yi sallah, Sarkin Muri Alhaji Abbas Tafida, ya baiwa fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar dazukan jihar Taraba , ko su daina garkuwa da mutane.

Wannan kalaman na basaraken ya jawo cece-kuce tsakanin jama'a duk da ana ganin cewa sarkin yayi jawabin ne a fusace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel