Manyan Masu Fada Aji Na Arewa Ke da Alhakin Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Matawalle Ya Fallasa
- Gwamna Matawalle na jihar Zamfara yace manyan masu fada aji a arewa suke da alhakin halin da yankin ke ciki
- Gwamnan yace babu kyakkyawan jagoranci a arewa domin kowa kudirinsa ya samu mulki
- A cewarsa, matsalar tsaro ta dabaibaye yankin, inda talauci ya karu da rashin abinci
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Lahadi, yace shugabannin arewa ke da alhakin matsalar tsaron da ya mamaye yankin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Matawalle ya yi wannan hangen ne yayin da yake gabatar da wata takarda mai taken "Yaki da yan bindiga a yankin arewa maso yamma: Ƙalubale da hanyar warware su" a wurin taron ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar marubutan arewa a Kaduna.
Yace shugabannin arewa suke da alhakin yanayin da yankin ke ciki, wanda ya haɗa da aikata manyan laifuka kamar fyaɗe, kisan mata da ƙananan yara, sace mutane, fashi da makami da sauran manyan laifukan da suka mamaye yankin.
A cewar gwamnan, arewa ta rasa kyakkyawan shugabancin da zai jagoranci gina yankin da magance matsalolinsa, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Ya kuma ƙara da cewa manyan masu faɗa a ji na yankin arewa ba su da wani kudiri face su samu damar ɗarewa kan mulkin siyasa.
Matsalar da Zamfara ke ciki
Matawalle yace lokacin da ya amshi mulki a 29 ga watan Mayu 2019, Zamfara ta riga ta shiga halin ƙaƙanikayi na rashin tsaro da ya shafe lokaci mai tsawo.
Gwamnan yace jihar bata da wani labari a kullum kwana sai na zubar da jini, wuta, sace-sace da kuma korar mutane daga mahallinsu musamman waɗanda ke rayuwa a yankunan karkara.
Gwamna Matawalle, wanda kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Magaji, ya wakilta, yace:
"Rikicin ya kawo karuwar talakawa da kuma rashin abinci, Zamfara ta kama hanyar rugujewa ta kowane ɓangare saboda tada zaune tsaye a yankunan karkarar mu da ma arewa baki ɗaya."
"Ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi sun zama gidan aikata ta'addancin yan bindiga duka da cewa an daina haƙar ma'adanai a yankunan."
Arewa ta rasa masu tallafawa
Gwamnan ya koka kan rashin masu taimakawa daga ɓangarorin yan siyasa, waɗanda ke amfani da wannan damar wajen cimma wani kudirinsu na siyasa.
Yace: "Dukkan mu munga yanda manyan kudu-gabas da kudu-yamma suka ɗauki mataki cikin haɗin kai a kan duk abinda ya taso a yankinsu."
"Munga yadda suke da manufa ɗaya kuma basu gajiyawa wajen kokarin kawo cigaba a yankinsu.
Matawalle ya yi kira ga manyan shugabannin yankin arewa da su farka daga baccin da suke, su haɗa kansu domin fuskantar duk wani ƙalubale.
Asali: Legit.ng