2023: Babu Wata Yarjejeniyar Miƙa Mulki Tsakanin Buhari Da Tinubu, In Ji Jigon APC

2023: Babu Wata Yarjejeniyar Miƙa Mulki Tsakanin Buhari Da Tinubu, In Ji Jigon APC

  • Osita Okechukwu, jigo a jam'iyyar APC ya ce babu wata yarjejeniya cewa Buhari zai mika wa Tinubu mulki a 2023
  • Okechukwu, shugaban VON, ya bayyana hakan ne yayin martani kan ikirarin da Rufai Hanga ya yi na cewa akwai wannan yarjejeniyar
  • Okechukwu ya kara da cewa Buhari ba mutum bane mai son yin yarjejeniya da mutane sai dai yana saka kyauta da tukwici

Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma shugaban muryar Nigeria, VON, Osita Okechukwu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai yi wani alkawarin mika mulki ga jagoran jam'iyyar Ahmed Bola Tinubu ba, Daily Trust ta ruwaito.

Wanda ya kafa tsohuwar jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), kuma shugabanta, Senator Rufai Hanga, a baya bayan nan ya ce 'akwai yarjejeniyar' da ke nuni da cewa Buhai zai mika mulki ga Tinubu a 2023.

2023: Babu Wata Yarjejeniya Tsakanin Buhari Da Tinubu, In Ji Jigon APC
Shugaba Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Hanga, wanda ya shugabanci daya daga cikin jam'iyyun da suka hadu suka kafa APC a 2014, ya ce wannan yarjejeniyar ce ta sa Tinubu ya cigaba da zama a APC bayan wa'adin Buhari na farko.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

Amma, Daily Trust ta ruwaito cewa Okechukwu ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa babu wannan yarjejeniyar, ya kara da cewa Buhari bai cika yin yarjejeniya da mutane ba.

Okechukwu ya ce:

"A matsayina na mamban tsohuwar jam'iyyar CPC, ban taba jin wannan yarjejeniyar ba, Shugaban kasa zai so ko bai cika yin yarjejeniya a hukumance ko akasin haka da kowa ba. Amma yana yaba kyauta da tukwici.
"Abin da na sani kawai shine ba domin wani matsala ta doka ba da Asiwaju ne zai zama mataimakin shugaban kasa.
"Domin shugabanin jam'iyyar mu suna gargadi kan tikitin Musulmi da Musulmi.
"Shugabannin jam'iyyar mu sun ce tikitin musulmi da musulmi irin ta Abiola da Kingibe a 1993 ba za ta yi aiki ba a yanzu domin abubuwa sun sauya a 2015. Idan Buhari da Tinubu suka yi takara, abin zai canja. Haka ne yasa aka zaci Farfesa Yemi Osinbajo a madadinsa."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel