Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu
- Ana ta samun sauye-sauye a sararin siyasar Najeriya gabanin babban zaben na 2023
- Ya zuwa yanzu, da alama jam'iyyar adawa ta PDP tana shan kaye inda yawancin jiga-jiganta suke sauya sheka zuwa APC
- Karin mambobin jam'iyyar adawar sun koma jam'iyya mai mulki a Ribas a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli
Jam’iyyar Peoples Democratic Party a jihar Ribas ta rasa manyan jiga-jiganta guda hudu a hannun jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli.
Masu sauya shekar, wadanda suka fito daga karamar hukumar Khana ta jihar sune Dumka Philip Rojas, tsohon shugaban majalisar dokokin Khana, Lekia Nwanikpo, tsohuwar mai kula da ayyuka na musamman, Dumbete Obegu, da kuma tsohon mashawarci na musamman ga shugaban majalisar Khana, Dum Ntorue, Leadership ta ruwaito.
A madadin Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wani jigo jam’iyyar APC na Ribas, Injiniya Chukwudi Dimkpa, ya karbi sabbin mambobin tare da yaba musu kan jajircewarsu, inda ya kara da cewa dukkansu za su more dama daidai da kowa kuma za a dama da su a jam’iyyar.
Rojas ya yi ikirarin cewa shi da sauran wadanda suka sauya sheka sun fice daga PDP ne saboda zargin nuna kiyayya ga gwamnatin jihar.
Ya ci gaba da bayyana cewa APC ta zama abin sha'awa a gare su saboda dimbin ayyukan ci gaba da nade-naden mukaman tarayya da aka ba jihar sakamakon kyakkyawan ayyukan ofishin Amaechi.
A wani labarin, fadar Shugaban kasa a ranar Talata ta fada wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da ta daina sa ran lashe babban zaben na 2023, saboda har yanzu talakawa za su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari mubaya'a kuma ba za su taba yin watsi da shi ba.
An zargi PDP da ba ‘yan Najeriya fatan karya cewa saboda rashin tabuka abin a zo a gani a jam’iyyar APC, a matakin kasa, cewa (PDP) za ta karbi mulkin da ta rasa a hannun APC a shekarar 2023, Daily Nigerian.
Amma Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, wanda ya yi magana jim kadan bayan Sallar Idi a Daura ta Katsina, ya ce ’yan Najeriya sun sani daram kuma ba za su yarda wani bangare ya karbi mulki a 2023 ba.
Asali: Legit.ng