Da Duminsa: Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC
- APC ta sha alwashin fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 wanda kowa zai amince da shi
- Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar, Sen. John Akpanudoehede, shine ya faɗi haka yayin martani ga PDP
- Ya ƙara cewa PDP na girbar abinda ta shuka a baya ne shiyasa take ganin APC ma zata yi haka
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa a lokacin da ya dace, zata fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na 2023 wanda kowa zai amince da shi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai
Sakataren kwamitin riƙon kwarya na jam'iyya mai mulki, Sen. John Akpanudoehede, shine ya faɗi haka a wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Jawabin ya yi martani ne game da zargin da PDP ta yi cewa shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya na son cigaba da mulki.
Sakataren APC ya jaddada cewa jam'iyya ba zata bar wasu ɗai-ɗaikun mutane su dinga juya gwamnatin shugaba Buhari yadda suke so ba, a dai dai lokacin da zaɓen 2023 ke gabatowa, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Zamu baiwa PDP mamaki
A cewar sakataren APC, bayan jam'iyyarsu ta yi gangamin ta na ƙasa zata baiwa jam'iyyar adawa PDP mamaki.
Yace: "Bayan babban taron mu na ƙasa, zamu basu mamaki (PDP) idan muka fitar da amintaccen ɗan takarar shugaban ƙasa kuma kowa ya amince da shi, wanda zai ɗaga tutar APC a zaɓen 2023."
"APC ba ta da kudirin zarcewa zango na uku a kan mulki kamar PDP, abinɗa muke yi yanzun shine ƙara kafa jam'iyya kuma ba zamu bar wasu ɗai-ɗaikun mutane su dinga juya gwamnatin mu ba."
Bamu da kuduri irin na PDP
Sakataren APC ya ƙara da cewa jam'iyyarsu ba kamar PDP bace domin yanzun PDP tana girban abinda ta shuka a baya ne.
Akpanudoedehe ya tuna cewa PDP ta so zarce wa a kan karagar mulki zango na uku lokacin da mulki ke hannunta.
KARANTA ANAN: Barka da Sallah: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Yan Bautar Kasa NYSC da Kyautar Kudi da Shanu a Daura
A cewarsa, APC ba ta da wannan shirin, kuma zata ba PDP mamaki idan ta kammala babban gangaminta na ƙasa wanda aka shirya farawa ranar 31 ga watan Yuli.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Yi Magana Kan Jirgin Yakin Sojojin Sama NAF da Ya Fado a Zamfara
Shugaban ƙasa, Buhari, ya nuna rashin jin daɗinsa da hatsarin jirgin yaƙin NAF a jihar Zamfara.
Buhari, wanda aka bashi labarin lamarin da ya faru a mahaifarsa Daura, yace ya kaɗu sosai da jin labarin.
Asali: Legit.ng