Kotu ta yanke wa direban masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar harbi

Kotu ta yanke wa direban masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar harbi

  • Kotu ta yankewa matashi hukuncin kisa bayan kama shi da hannu a garkuwa da wata mata
  • An kama matashin da laifin hada kai tare da yin garkuwa da matar wani hamshakin dan kasuwa a Bayelsa
  • A gefe guda kuma kotun ta sallami wani matashi tare da wanke shi daga irin wannan zargin

Wata babban kotu a Jihar Bayelsa, da ke zamanta a Yenagoa, ta yanke wa wani matashi dan shekara 39, Charles Nikson, hukuncin kisa ta hanyar harbi, The Punch ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama shi da laifin hada kai a garkuwar da a kayi da Alex Iliemokumo da Vivian Okoye, matar wani mashahurin dan kasuwa kuma ma'aikacin lafiya a Jihar Bayelsa a cikin watan Nuwambar 2020.

Taswirar jihar Bayelsa
Taswirar jihar Bayelsa. Hoto. The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa a Kebbi Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Don Yaƙar Ƴan Bindiga

Okeye, matar Obinna Okeye, wanda aka fi sani da Blessed Obaino mamallakin shagunan A-Z Electronics a sassa mabambanta na Yenagoa, da kuma ma'aikacin lafiya da aka fi sani da Alex Ogregade Ileimokumo daga yankin Igbedi na karamar hukumar Southern Ijaw, an ceto su bayan an yi musayar wuta da jami'an Operation Puff Adder.

Nikson, wanda shine direban tawagar yan garkuwar, an gurfanar da shi a gaban babbar kotun Ogbia bisa tuhuma guda biyu ta farko zargin hadin kai wajen aikata laifi sai kuma garkuwa da mutane.

An gurfanar da shi a kotun tare da wani da ake zargi, David Ekegima. An sallami Ekegima tare da wanke shi.

KU KARANTA: Ango ya fasa aure saboda abinci, ya kuma auri wata a ranar bikin

Babbar mai shari'a, Justice Raphael Ajunya, lokacin da take hukunci a kan lamarin, ta kama Nikson da laifukan guda biyu.

A cewar ta: "zargin hada kai da yan ta'adda, babu takamaman hukunci. saboda haka na yanke ma hukuncin shekara 10 a gidan yari."

An yi harbe harbe sosai a watan Nuwamba, 2020 tsakanin jami'an Operation Puff Adder na rundunar yan sanda da kuma tagawar wasu masu garkuwa da mutane su bakwai a hanyar Iminringi ta karamar hukumar Ogbia, wanda ya yi sanadiyyar ceto Vivian Okoye.

Mafarauta sun ɗirkawa mai garkuwa harsashi ya mutu wurin karɓar kuɗin fansa

A wani labarin daban, mafarauta sun harbe wani mutum da ke cikin gungun masu garkuwa da mutane uku har lahira yayin da ya tafi karbar kudin fansa a kauyen Abobo a karamar hukumar Okehi na jihar Kogi, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mafarauci da ke cikin wadanda suka shirya atisayen, ya ce an yi harbin ne misalin karfe 5.23 na asubahi a ranar Talata.

Mutumin ya fito ne daga wurin da ya ke boye a yankin Abobo, bayan Itakpe, wasu yan kilomita kadan daga babban titi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel