Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa a Kebbi Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Don Yaƙar Ƴan Bindiga

Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa a Kebbi Sun Sadaukar Da Rabin Albashinsu Don Yaƙar Ƴan Bindiga

  • Masu rike da mukaman siyasa a jihar Kebbi sun bada rabin albashinsu na Yuni don yaki da yan bindiga
  • Babale Yauri, sakataren gwamnatin jihar Kebbi ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin a Birnin Kebbi
  • Yauri ya ce wannan karamcin zai taimaka wurin yaki da kallubalen rashin tsaron yana mai neman hadin kan jama'ar jihar

Masu rike da mukaman siyasa a jihar Kebbi sun sadaukar da rabin albashinsu na watan Yuni ga gwamnatin jihar domin bada gudunmawa wurin yaki da 'yan bindiga a jihar, News Wire ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar, Babale Yauri ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Birnin Kebbi.

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Zamfara baki ɗayansu za su bi Matawalle zuwa jam'iyyar APC, Hadimin Gwamna

Da ya ke magana, Yauri ya ce:

"Wannan matakin ya zo a lokacin da ya dace domin kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar da Nigeria baki daya.
"Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da sauran hukumomin tsaro suna aiki babu kakkautawa domin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.
"Wannan karamci da kuma gudunmawa daga bangarenmu domin ganin munyi maganin wannan mummunan kallubalen da ke adabar mu."

Yauri ya kara da cewa bai kamata a bar wa hukumomin tsaro da gwamnati komai ba game da yaki da kallubalen tsaron.

KU KARANTA: Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano

Sakataren gwamnatin ya jadada muhimmancin da ke da akwai wurin ganin an samu hadin kai da zaman lafiya a jihar domin shine zai haifar da cigaba a jihar da kasa.

Kebbi na daya daga cikin jihohin da yan bindiga ke adaba a yankin arewa. Yan bindigan sun halaka mutane da dama tare da garkuwa da wasu.

A farkon watan Yuni, an sace kimanin dalibai da malamai 94 da rana tsaka a makarantar gwamnati da ke Birnin Yauri a Kebbi.

Gwamnatin Kaduna ta yi magana kan zanga-zangar da ɗalibai suka yi a Kwalejin Gidan Waya

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana jiran cikaken rahoto a kan zanga-zangar da daliban Kwallejin Ilimi na Gwamnatin Kaduna da ke Gidan Waya suka yi.

Sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Litinin ya ce a halin yanzu rahoton da gwamnati ta samu shine dalibi daya ya rasu, wasu sun jikkata sannan jami'an tsaro uku sun samu rauni.

Gwamnatin ta kuma ce bata tura jami'an tsaro makarantar domin su musgunawa masu zanga-zanga ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164