Ango ya fasa aure saboda abinci, ya kuma auri wata a ranar bikin

Ango ya fasa aure saboda abinci, ya kuma auri wata a ranar bikin

  • Wani ango ya janye daga aure ranar biki saboda ba a kammala wani abincin ba
  • Iyalan ango Ramakant Patra ne suka bukaci nama, abun da ya janyo hargitsi har ta kai ango ya fasa auren
  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da angon ya yi auren a daren da wata matar daban kafin komawarsa gida

Wani matashi ya fasa auren budurwar sa a ranar biki bayan iyalan amarya sun gaza kammala abinci a Sukinda ranar Laraba, Guardian Ng ta ruwaito.

Kamar yadda jaridar The New Indian Express ta ruwaito, angon dan shekara 27, mai suna Ramakant Patra, ya auri wata matar a yakin kafin ya koma gida.

Amarya da Ango
Amarya da Ango wurin daurin aure. Hoto: Digest Nigeria
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamna Bala Mohammed sun mamaye birnin Kano

Patra, mazaunin Rebanapalascal da ke makwabtaka da Keonjhar, ya isa kauyen Bandhagon unguwar Sukinda da iyalan shi don daura masa aure a ranar Laraba, India.com ta ruwaito.

Sanadin fasa auren

Bayan isar su gidan, sun samu tarba daga iyalan amarya kuma bayan kammala al'adun da suka dace, an dauke su zuwa teburin cin abinci don cin abincin rana.

Kafin a zuba abincin, mahalarta bikin suka bukaci nama. Bayan sun fahimci babu, iyalan sun shiga cacar baki tsakanin su da dangin amarya da masu raba abinci.

Lamarin ya munana kuma an gaza shawo kansa. Da Patra ya san cewa ba a dafa nama a shagalin ba, sai ya dakatar da auren ya bar kowa da mamaki.

KU KARANTA: Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura

Duk da rokon da dangin amarya suka yi da kokarin shawo kansa, amma abun ya gagara don tuni ango ya fice shi da iyalan sa.

Patra ya wuce gidan wasu yan uwansu a kauyen Gandhapala da ke Panchayat a Sukinda inda suka kwana a nan.

Angon ya auri wata a ranar

Daga bisani ya auri wata matar a Phulajhara da ke Tamka a wannan ranar kafin komawa Keonjhar, majiyoyi sum ce. Ba a shigar da korafi gaban yan sandan da ke da hurumi ba. Wannan dadaddiyar dabi'a ce da ango da iyalan shekaru da dama da suka gabata.

A wani labarin daban, gwamnoni da ministoci a halin yanzu sun isa fadar mai martaba Sarkin Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren Yusuf Buhari, dan shugaban kasa, Daily Trust ta ruwaito.

A yanzu haka Yusuf na shirin auren diyar Sarkin Bichi kuma tawagar da ke karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa suna Kano don tsara tsare-tsaren bikin auren.

Sarkin na Bichi kane ne ga Sarkin Kano, wanda a yanzu haka shi ke karbar bakuncin wakilai daga fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel