Mafarauta sun ɗirka wa mai garkuwa harsashi ya mutu yayin da yazo karɓar kuɗin fansa
- Mafarauta sun bindige wani mai garkuwa da mutane a yayin da ya zo karbar kudin fansa a Kogi
- Abdulraheem Ohiare Ozovehe, shugaban karamar hukumar Okehi inda abin ya faru ya jinjinawa mafarautar
- Rundunar yan sandan jihar Kogi ta bakin kakakinta ta, DSP Williams Ovye Aya, ta tabbatar da afkuwar lamarin
Mafarauta sun harbe wani mutum da ke cikin gungun masu garkuwa da mutane uku har lahira yayin da ya tafi karbar kudin fansa a kauyen Abobo a karamar hukumar Okehi na jihar Kogi, Daily Trust ta ruwaito.
Wani mafarauci da ke cikin wadanda suka shirya atisayen, ya ce an yi harbin ne misalin karfe 5.23 na asubahi a ranar Talata.
DUBA WANNAN: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina
Mutumin ya fito ne daga wurin da ya ke boye a yankin Abobo, bayan Itakpe, wasu yan kilomita kadan daga babban titi.
Nan take daya daga cikin mafarautar ya bude masa wuta ya halaka shi. Mafarautan sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su a wurin.
An dauki gawar wanda ya mutun da bindigarsa an mika wa yan sanda a Okehi.
Mafarautan sun bi cikin dajin domin farautar sauran masu garkuwan da suka yi wa rauni da harsashin bindiga.
Shugaban karamar hukumar ya jinjinawa mafarauta
Premium Times ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Okehi, Abdulraheem Ohiare Ozovehe, ya ziyarci wurin da abin ya faru ya jinjinawa mafarautan.
Shugaban karamar hukumar ya bukaci mutanen garin su cigaba da bawa mafarautar goyon baya da hadin kai domin magance masu garkuwar.
KU KARANTA: Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura
Ya jadada cewa gwamnatinsa za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa don kiyaye lafiya da rayyukan mutane da dukiyoyinsu.
Kakakin yan sandan jihar Kogi DSP Williams Ovye Aya, ya ce ya san da afkuwar lamarin amma ya ce zai tuntubi DPO na yankin Okehi domin samun karin bayani.
Asali: Legit.ng