Tsadar Abinci: CBN Ta Kawo Mafita, Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya

Tsadar Abinci: CBN Ta Kawo Mafita, Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya

  • Babban Bankin Najeriya ya bayyana kudurinsa na karya farashin shinkafa a fadin kasar
  • Ya ce zai fitar da tan miliyan tara na shinkafa domin sayarwa masu sarrafa shinkafa a kasar
  • Bankin ya ce wannan na zuwa ne a kokarinsa na samar da wadataccen abinci ga 'yan Najeriya

A kokarinsu na samar da wadataccen abinci ga 'yan Najeriya tare da karya farashin shinkafa, Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya, sun fara batun kaddamar da sayar da tan miliyan tara na tallafin shinkafa ga masu sarrafata.

Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele yayin da yake kaddamar da shirin sayarwar da kuma fara noman rani a Kaduna ya ce, bankin a shirye yake ko yaushe don tallafawa harkar noma, The Nation ta ruwaito.

Ahmed Mohammed na CBN reshen jihar wanda ya wakilci gwamnan, ya ce shirin an shirya shi ne don sayar da shinkafar a kan farashi mai rahusa da nufin karya farashin don amfanin kowa a Najeriya da ma wasu kasashen.

KU KARANTA: Obasanjo Ya Yi Gargadin Matsalar da Najeriya Za Ta Shiga Saboda Yawan Haihuwa

Tsadar Abinci: CBN Za Ta Karya Farashin Shinkafa a Najeriya, Ta Bayyana Mafita
Wasu daga nau'ikan shinkafa da ake amfani dasu | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamnan Babban Bankin ya ce, bankin a shirye yake domin tabbatar da wadatar abinci da inganta noman shinkafa a kasar.

A cewarsa:

"Wannan shirin shiri ne na kasa baki daya da nufin samar da abinci ga kowa, shi ya sa Babban Bankin a ko yaushe a shirye yake ya tabbatar akwai kudade ga manoma."

Wakilin Daraktan Habaka Kudi na Babban Bankin, Mista Chika Nwaja, ya ce Bankin na da aniyar cire batun ‘yan tsakiya daga sayar da shinkafa ga masu sarrafawa don 'yan Najeriya su saya a farashi mai rahusa.

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar Manoman Shinkafa ta kasa (RIFAN), Alhaji Aminu Goronyo, ya ce duk abin da ke faruwa a wurin taron shi ne Babban Bankin wanda ya amince da hakan don kawai ciyar da kasar nan gaba.

A cewarsa,:

"Duk da matsalolin tsaro, manoman shinkafa na kokarin samar da shinkafa ga kasar."

Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), ta ce noman shinkafa a kasar ya karu daga tan miliyan biyu a 2015 zuwa tan miliyan tara a 2021, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake bayyana hakan a Kaduna a ranar Alhamis, Shugaban RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce duba da yawan kayan da ake sarrafawa a yanzu, Najeriya ta shirya zama kasar da zata ke fitar da shinkafa zuwa kasashen waje.

A cewarsa:

“Kafin zuwan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, mun saba samar da kimanin shinkafa tan miliyan biyu a shekara.
“A yau, za mu iya alfahari da tan miliyan tara a shekara; akwai bambanci sosai kuma yanzu za mu iya cewa balo-balo Najeriya ta wadatu da shinkafa.''

KU KARANTA: Lale Maraba: Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC

Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar

A wani labarin, Masoyan Gurasa, sanannen abinci ga mutan Kano, na iya shiga mawuyacin hali domin kuwa masu sarrafa shi suna barazanar daina samar da shi saboda hauhawar farashin garin fulawa; babban sinadari don samar da gurasa.

Gurasa shine burodin gargajiya wanda akafi sani a tsakanin mutanen Kano kuma ana siyar dashi a yankuna da yawa ciki da wajen babban birni.

Hakanan mutane a wasu jihohin arewacin suma suna gudanar da kasuwancinsa duk da cewa ba za su iya daidaita dandano da kimarsa da na jama'ar Kano ba kasancewarsa abinci mai daraja da dinbin tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel