Obasanjo Ya Yi Gargadin Matsalar da Najeriya Za Ta Shiga Saboda Yawan Haihuwa

Obasanjo Ya Yi Gargadin Matsalar da Najeriya Za Ta Shiga Saboda Yawan Haihuwa

  • Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana damuwar da Najeriya za ta iya shiga nan gaba
  • A cewarsa, yawan da 'yan Najeriya ke dashi a yanzu ba karamin abun damuwa bane nan da 2050
  • Ya ce dole ne a san yadda za a yi a sarrafa yawan 'yan Najeriya ko kuma kasar ta zama mafi yawan mutane a duniya

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce karuwar yawan mutane a Najeriya na iya zama matsala idan ba a sarrafa hakan da kyau ba, The Cable ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan gargadin ne yayin da yake magana a wani taro a jihar Ogun ranar Lahadi.

A farkon wannan watan, Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto wanda ya kiyasta cewa yawan mutanen Najeriya ya haura miliyan 211.

KU KARANTA: PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

Yawanmu zai zama mana damuwa nan gaba, Obasanjo ya bayyana matsakar yawan 'yan Najeriya
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo | Hoto: newstage.com.ng
Asali: UGC

Da yake mayar da martani, Obasanjo ya yi hasashen cewa idan ba a dakile yawan mutanen ba, Najeriya za ta zama kasa ta uku mafi girma a duniya a shekara ta 2050.

Ya kara da cewa dole ne kasar ta rungumi "kula da yawan jama'a" cikin sauri domin dakile wani mummunan sakamako na karuwar yawan 'yan kasa.

Tsohon shugaban kasar ya ce:

“Mun tashi daga miliyan 120 zuwa sama da miliyan 200, mun kara adadin yawan Faransawa zuwa yawanmu, kuma idan muka ci gaba da yadda muke tafiya, nan da shekara ta 2050, za mu zama kasa ta uku mafi girma a duniya."
“Idan muka ci gaba a haka, zuwa shekara ta 3000, za mu zama babbar kasa a duniya. Yanzu, me za mu yi don magance lamarin? Ta yaya za mu magance wannan yawan?

Da yake jayayya kan cewa yawan na iya zama wata kadara ko kuma jidali, dattijon ya ce idan har al'umma ba ta shirya tsaf ba to kasar za ta dandana kudarta a yanzu da kuma nan gaba, Channels Tv ta ruwaito.

“Abin da ya kamata mu yi shi ne ilmantuwa game da kula da yawan jama’a. Wasu mutane ba sa son ambatan tsarin iyali, amma duk abin da za ku yi, dole ne ku sarrafa yawanku don amfanin duk abinda ke zaune a cikin al'ummar ku."

KU KARANTA: Lale Maraba: Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC

Tsohon shugaba Jonathan ya magantu kan abinda ke jawo aikata laifuka a Najeriya

A wani labarin daban, Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya koka kan karuwar aikata laifuka a kasar yana mai cewa galibinsu shan miyagun kwayoyi ne ke jawo su.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi tir da bayyanar kungiyoyin asiri a makarantun sakandare da firamare A cewarsa, wannan ba karamin abin takaici bane saboda ya kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Jonathan yace:

"Yanzu muna da kungiyoyin asiri a makarantun firamare da sakandare, a baya ya tsaya a manyan makarantu, amma yanzu zaku ga yara a wadannan makarantun suna tunanin yadda za su kashe sa'anninsu, wannan abin bakin ciki ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.