Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar

Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar

  • Masoya Gurasa a jihar Kano da alamun za su yi sallama da cin Gurasa saboda wasu dalilai
  • Kungiyar masu sarrafa Gurasa sun ce za su daina sana'ar saboda hauhawar farashin garin fulawa
  • Sun koka kan yadda kaya ke tashi a kasuwa ba gaira ba dalili, kuma sukan yi asara da dama

Masoyan Gurasa, sanannen abinci ga mutan Kano, na iya shiga mawuyacin hali domin kuwa masu sarrafa shi suna barazanar daina samar da shi saboda hauhawar farashin garin fulawa; babban sinadari don samar da gurasa.

Gurasa shine burodin gargajiya wanda akafi sani a tsakanin mutanen Kano kuma ana siyar dashi a yankuna da yawa ciki da wajen babban birni.

Hakanan mutane a wasu jihohin arewacin suma suna gudanar da kasuwancinsa duk da cewa ba za su iya daidaita dandano da kimarsa da na jama'ar Kano ba kasancewarsa abinci mai daraja da dinbin tarihi.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kame tsagerun IPOB 60 dake kai hare-hare da kone ofisoshin INEC

Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar
Shahararren Abincin Kanawa, Gurasa | Hoto: universalreportersng.com
Asali: UGC

Hajiya Amina Abubakar, shugabar kungiyar masu sana’ar Gurasa a Kano, ta ce farashin garin fulawa yana yin tashin gwauron zabi a kowace rana kuma ci gaba da kasuwancin ya zama musu mai wahala sosai.

Ta koka da cewa:

“Farashin da kuka sayi garin fulawa da safe ya bambanta da wanda kuke saya da yamma.
“Duk da cewa ba mu da wata hanyar samun kudin shiga, kasancewar yawancinmu zawarawa ne tare da marayu masu rauni, ya fi kyau mu dakata fiye da ci gaba da gudanar da kasuwancin a mawuyacin yanayi irin wannan.
"Yanzu, yawancinmu ba mu da jari, kamar yadda wasu aka shigar dasu kara kotu kan wani bashi da ake binsu. Don haka kawai muke gudanar da kasuwancin a cikin tafka asara."

Hajiya Amina ta kara da cewa tun da farko mambobin sun dauki wasu tsauraran matakai don ci gaba da kasancewa a cikin kasuwancin ciki har da rage girman Gurasan amma hakan bai samar da sakamakon da ake nema ba.

Ta ce baya ga sayen fulawar kan farashi mai tsada, suna kuma kokawa game da batun lalata garin fulawar kasancewar bashi da auki.

Sakataren kungiyar, Ahmad Rufa’i Tanko ya ce halin da ake ciki ya jefa wasu mambobinsu cikin bashi.

Kungiyar masu sana'ar Gurasa sun nemi tallafi kada kasuwancinsu ya durkushe

Kungiyar ta yi kira ga hukumar da abin ya shafa da ta duba matsalarsu tare da ceto kasuwancinsu daga durkushewa.

Sai dai, Sakataren Kungiyar Masu Sayarda Gurasa, Hadiyatullah Muhammaad, ya shawarci masu yin Gurasa da su yi tunani mai zurfi da nufin ceto kasuwancin nasu.

Mazauna yankin, wadanda suka zanta da jaridar Kano/Jigawa a kan batun, sun yi kira ga gwamnati da ta sa baki saboda ba za su iya jure rasa hanyar samun abinci ba.

Hajiya Rabi Sani da Malam Ibrahim Muhammad, masu amfani da Gurasa a kai a kai, sun ce rufe kasuwancin zai yi matukar shafarsu.

Lokacin da aka tuntube shi, wani babban dillalin garin fulawa a mashahuriyar Kasuwar Singer, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya zargi tsadar garin fulawar ga hauhawar farashi wanda kuma ya shafi sauran kayayyaki a kasuwar.

KU KARANTA: Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar dokoki ta kasa

Mai kamfanin BUA, Abdul Samad Rabi'u ya gwangwaje jihohi 4 da tallafin biliyoyi

A wani labarin, Kungiyar Abdul Samad Rabiu Africa Initiative (ASR Africa) ta ce za ta bayar da tallafin Naira biliyan 10 don ayyukan kiwon lafiya a jihohi hudu - Ogun, Sokoto, Kwara da Edo.

Ubon Udoh, manajan darakta na ASR Afirka, ya ce za a ba da sabon tallafin ne kan ayyukan kula da lafiya daga kiwon lafiyar mata da yara zuwa kayayyakin kiwon lafiya, bunkasa aiki, da sauransu, The Cable ta ruwaito.

Wani bangaren jawabin Mista Udoh yana cewa:

"ASR Afirka a yanzu ta yanke shawarar bada N2.5bn ga kowace jiha cikin jihohi hudu a Najeriya - Ogun, Kwara, Sokoto da Edo."

Asali: Legit.ng

Online view pixel