Lale Maraba: Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC

Lale Maraba: Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC

  • Gwamnan jihar Zamfara ta tabbata ya bar PDP zuwa APC; jam'iyya mai mulkin tarayya
  • An ruwaito cewa, gwamnonin APC 18 ne za su yi maraba da gwamnan tare da sauran jiga-jigai
  • Majiyoyi sun bayyana cewa, gobe ne gwamnonin za su yi liyafar karbar gwamnan zuwa APC

Rahotanni sun tabbatar da cewa, gwamnan jihar Zamfara Matawalle zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC gobe.

A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar The Nation ya ce, mai magana da yawun gwamnan, Mista Yusuf Idris, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya cewa gwamnonin APC 18 za su yi maraba da shi.

KU KARANTA: Bayan Gwamna Matawalle, Jigo a Jam'iyyar APGA Ya Bi Sahu Zuwa Jam'iyyar APC

Ya bayyana cewa:

"Yanzu an gama komai domin gwamnanmu ya sauya sheka daga PDP zuwa APC."

A cewarsa, gobe za a yi kasaitaccen liyafa a Gusau, babban birnin jihar.

Lale Maraba: Gobe Gwamnoni 18 Za Su Karbi Matawalle Zuwa Jam'iyyar APC
Gwamnan Zamfara tare shugaban kasa | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Idris ya ce

"Gwamnan zai zo tare da dukkan mambobin majalisar kasa da na jihar gami da shugabannin jam'iyyar PDP daga dukkan matakan jihar."

Yayi imanin ficewar gwamnan zai karfafa jam'iyyar APC a jihar.

“‘Yan siyasar Zamfara sun kasance 'yan gida daya kuma a matsayinsa na gwamnan PDP, yana da kyakkyawar alaka da wadanda ke cikin jam’iyyun adawa.
“Mutane da yawa daga manya har kanana sun bi gwamnan zuwa PDP domin bayar da shawarwarinsu na kwarai don ci gaban jihar.
"Wasu daga cikin irin wadannan an ba su manyan mukamai da matsayi na gwamnati wadanda suka rike su da kyau."

Matawalle zai kasance gwamnan PDP na uku da ya fice daga jam’iyyar ya koma APC, in ji PM News.

Sauran wadanda suka sauya shekar sun hada da Gwamna Dave Umahi na Ebonyi da Ben Ayade na Kuros Riba.

Tare da ficewar Matawalle, adadin gwamnonin PDP ya ragu daga 16 zuwa 13. APC yanzu tana da jihohi 23 a karkashin ikonta.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Harbe Mata Mai Juna Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Mijinta

PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

A wani labarin, Majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a gobe zai koma jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan yasa PDP ta ce za ta dauki matakin doka domin dakatar da gwamnan na Zamfara daga barin jam'iyyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba, an tattaro cewa za a ambaci karar da wasu jiga-jigan PDP suka shigar kan sauya shekar Matawalle a yau a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel