Karin kudi a Najeriya yayinda FG, jihohi da kananan hukumomi suka raba N605.9bn a tsakaninsu a watan Mayu

Karin kudi a Najeriya yayinda FG, jihohi da kananan hukumomi suka raba N605.9bn a tsakaninsu a watan Mayu

  • Jimlar N605.958bn aka raba a tsakanin kananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya a matsayin kason Mayu
  • A cewar kwamitin rabon, FG ta karbi N242.120bn, jihohi sun samu N194.19bn yayin da kananan hukumomi suka samu N143.742bn
  • A halin yanzu, kudaden shiga da aka samu a cikin watan Mayu ya yi kasa da na watannin baya a cewar rahotanni

Gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da majalisun kananan hukumomi za su samu kudi don aiwatar da wasu ayyukan su tare da biyan albashi biyo bayan raba kason da gwamnatin tarayya ta yi na watan Mayu.

Wannan na zuwa ne yayin da kwamitin rabo na asusun Tarayya ya raba kudin ga bangarorin gwamnati guda uku.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: An nada Alkalan Shari'a 34 a jihar Kano bayan gwaji

Karin kudi a Najeriya yayinda FG, jihohi da kananan hukumomi suka raba N605.9bn a tsakaninsu a watan Mayu
Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba N605.9bn a tsakaninsu a watan Mayu Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya ta karbi biliyan N242.120, jihohi kuma sun samu biliyan N194.19, sannan kuma majalisun kananan hukumomi sun samu biliyan N143.742, yayin da jihohin da ke samar da mai suka samu N26.901bn a matsayin rarar man fetur, jaridar The Punch ta ruwaito.

Wadannan sun bayyana ne a cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Charles Nwodo ya fitar a Abuja, in ji The Guardian.

Sanarwar da kwamitin ya bayar a karshen taron ya nuna cewa Babban Harajin da ake samu daga Harajin kaya a watan Mayu ya kai N181.078bn sabanin N176.710bn da aka rarraba a watan Afrilu, wanda ya haifar da karin N4.368bn.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun damke wata amarya da ta aika mijinta barzahu a Jigawa

Ya zayyana rabon kamar haka: Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 25.260, Jihohi kuma sun samu Naira biliyan 84.202, sai kuma Kananan Hukumomin da suka samu Naira biliyan 58.941.

Kudaden da aka raba na harajin N428.198bn da aka samu na watan ya yi kasa da N497.385bn da aka samu na watan da ya gabata da N69.197bn.

Daga wannan ne, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 175.541, jihohi suka samu N89.037bn, kananan hukumomi suka samu N69.644bn, kuma kashi 13 cikin 100 na kudin shiga daga ma’adinai sun samu N24.666bn.

A cewar sanarwar, Harajin Kamfanoni, da matatun Mai da Gas, harajin shigo da kaya ya ragu, yayin da VAT ya karu a gefe.

Hakanan ya bayyana cewa jimillar kudin shigar da aka raba na N605.958bn a watan Mayu ya hada da kudaden haraji na N357.888bn, VAT na N168.403bn, harajin ma’adinai na N7.940bn, rarar chanjin kudaden waje na N1.727bn, da kari da na mai ba na N70bn.

A wani labarin, Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yayi ƙarin haske kan bashin da gwamnatin yanzu ke amso wa, yace akwai buƙatar rance matuƙar ana son cigaba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ana ta cece-kuce da sukar gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan yawan ƙarɓo bashin da take yi, ana ganin tana ƙoƙarin lalata goben yan Najeriya musamman masu taso wa.

Amma da yake fira da hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN), Fashola yace gwamnatin Najeriya ba zata iya kawo cigaba ba matuƙar ba ta karɓo bashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel