‘Yan sanda sun damke wata amarya da ta aika mijinta barzahu a Jigawa

‘Yan sanda sun damke wata amarya da ta aika mijinta barzahu a Jigawa

  • An damke wata amarya mai shekaru 25 a jihar Jiawa, Hadiza Musa kan zargin aika maigidanta barzahu
  • Lamarin ya faru ne a yammacin Talata a kauyen Maradawa da ke karamar hukumar Kazaure inda wacce ake zargin ta buga wa mijin nata tabarya
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da kamun matar inda tace za a aikata kotu da zaran an kammala bincike

‘Yan sanda a jihar Jigawa sun cafke wata mata mai shekara 25, Hadiza Musa kan zargin aikawa da mijinta barzahu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamun kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun kai farmaki wani gari a Kaduna, sun jikkata mutum 12 tare da halaka daya

‘Yan sanda sun damke wata amarya da ta aika mijinta barzahu a Jigawa
Amarya ta aika mijinta barzahu bayan sabani ya gibta tsakaninsu a Jigawa Hoto: nigeriantribuneng.com
Asali: UGC

Ya ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata a kauyen Maradawa da ke karamar hukumar Kazaure.

Sashin Hausa na BBC ma ta ruwaito cewa rundunar yan sandan ta ce ta fara gudanar da bincike kan matar da ake zargin ta aikata wannan laifin bayan wata hatsaniya ta barke a tsakaninsu.

Adam ya ce wanda abun ya cika da shi ya samu rauni a kansa wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Ya ce an kai mamacin babban asibitin Kazaure inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Sabon rikici ya kunno kai a PDP yayinda kotu ta tsige Shugaban jam’iyyar

"Ana gudanar da bincike a kan lamarin kuma za a tura shi kotu," in ji shi.

A wani labarin kuma, rahotanni daga jaridar Katsina Post sun bayyana cewa wani mutumi ya cafke abokinsa tunbur haihuwar uwarsa, ya shiga gidansa ya na neman matarsa ta aure.

Kamar yadda muka samu labari, wannan Bawan Allah ya yi ram da amininsa a gidansa, ya je kwartanci, wannan lamari ya auku a unguwar Modoji, jihar Katsina.

Jaridar ta ce ta sakaya bayanan da suka shafi wadannan mutane domin a tsare masu mutuncinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel