Da dumi-dumi: An nada Alkalan Shari'a 34 a jihar Kano bayan gwaji
- Babban Alkalin Jihar Kano, Mai Shari’a Nura Sagir, ya amince da nadin karin alkalai 34 a kotunan Musulunci da ke Jihar
- An amince da nadin alkalan ne bayan sun ci jarabawar da Hukumar Kula Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta gudanar
- Za a rantsar da wadanda aka nada a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, a babbar kotun jihar
Da amincewar Mai Shari’a Nura Sagir, babban alkalin Kano, an kara wasu alkalai 34 na kotun shari’ar Musulunci a jihar a ranar Alhamis, 24 ga watan Yuni.
Kakakin ma’aikatar shari’ar jihar, Baba Jibo-Ibrahim ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun damke wata amarya da ta aika mijinta barzahu a Jigawa
Jibo-Ibrahim a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa Babban Alkalin ya amince da nadin alkalan ne bayan sun ci jarabawar da Hukumar Kula Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta gudanar, jaridar Aminiya ta ruwaito.
Kakakin ya kara da cewa za a rantsar da wadanda aka nada a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni, a babbar kotun jihar.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun kai farmaki wani gari a Kaduna, sun jikkata mutum 12 tare da halaka daya
Ya ce:
“Ana bukatar sabbin Alkalan Kotunan Shari’ar Musuluncin da za a rantsar ranar Juma’a 25 ga watan Yuni 2021 da su hallara a Babbar Kotu da misalin karfe 10.00 na safe.”
A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ranar Talata, ya sha alwashin ƙarasa aikin hanyar Gorondutse – Jakara wadda tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso ya fara, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Hanyar wadda ta taso daga Gorondutse/Aminu Kano zuwa jakara an raɗa mata suna 'Sheikh Mahmud Salga' kuma gwamnatin tsohon gwamna, Rabi'u Kwankwaso ce ta fara aikin a zangon mulki na biyu.
Ganduje ya ɗauki wannan alƙawari ne yayin buɗe biki da aka yi wa take da 'Makon tsaftace jihar Kano' a Jakara.
Asali: Legit.ng