Dalilin da Yasa Najeriya Take da Buƙatar Cigaba da Karɓo Bashi, Fashola

Dalilin da Yasa Najeriya Take da Buƙatar Cigaba da Karɓo Bashi, Fashola

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa take karɓo bashi da kuma abinda take yi da shi
  • Ministan ayyuka da gidaje, Babajide Fashola, ya bayyana cewa ƙasahen duniya da haka suka gina kansu
  • Ministan yace bashin da ake amso wa ba zai lalata goben yan Najeriya ba, sai dai ya gyara

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yayi ƙarin haske kan bashin da gwamnatin yanzu ke amso wa, yace akwai buƙatar rance matuƙar ana son cigaba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ana ta cece-kuce da sukar gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan yawan ƙarɓo bashin da take yi, ana ganin tana ƙoƙarin lalata goben yan Najeriya musamman masu taso wa.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Buƙaci Kamfanin MTN Ya Rage Farashin 'Data' Ga Yan Najeriya

Amma da yake fira da hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN), Fashola yace gwamnatin Najeriya ba zata iya kawo cigaba ba matuƙar ba ta karɓo bashi ba.

Misitan ayyuka, Babatunde Fashola
Dalilin da Yasa Najeriya Take da Buƙatar Cigaba da Ciyo Bashi, Minista Hoto: dailytimes.ng
Asali: UGC

Yace: "Muna da buƙatar gwamnati ta rinƙa ciwo ba shi domin zuba su a ɓangaren kawo cigaba da samar da abubuwan more rayuwa, waɗanda suke samar da aikin yi."

"Bana goyon bayan karbo bashi hakanan, amma ya kamata mu fahimci alfanun rancen."

"Idan zamu cigaba da rancen kuɗi domin zuba su a fannin da ya dace kuma mukayi hakan, to wannan mahawarar ba zata taɓa ƙarewa ba koda zamu kai safiya, kuma bana tunanin cewa ba zan yi nasara ba."

"Abu ne mai kyau kowa ya sanya idonsa a kan bashin da gwamnati ke karɓo wa, kuma me take yi da su. Kwanan nan muka ƙaddamar da wani aikin layin dogo a ma'aikatar sufuri, wannan aikin shekara 100 ne muka gama yanzun." inji shi.

KARANTA ANAN: Zan Saka Wa Yan Najeriya Saboda Ƙaunar da suke Nuna Mun, Buhari Yayi Jawabi a Fadar Shehun Borno

Manyan ƙasashen duniya sun dogara ne da bashi

Da yake bada misali da manyan ƙasashen da suka gina tattalin arziƙi mai ƙarfi ta hanyar rance, Fashola yace bashin da FG ke karɓo wa ba zai lalata goben yan Najeriya ba

Yace: ""Ƙasashen da suka fi cin bashi a duniya sun fito ne daga yammaci, amma da wannan bashin suka gina tattalin arziƙi mai ƙarfi, layin dogo, manyan filayen jirgin sama, makarantu da asibitoci."

"Kunsan wani abu? Mu ne muke zuwa mu yi amfani da waɗannan abubuwan, kuma dole sai mun biya kuɗi."

A wani labarin kuma PDP Ta Ragargaji APC a Zaɓen Cike Gurbin da Aka Gudanar a Jihar Kaduna

INEC ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbin da ta gudanar a mazaɓar Tudun Wada, Zaria, jihar Kaduna, kamsr yadda vanguard ta ruwaito.

Baturen zaɓen yankin, Dr. Muhammed Musa, ya bayyyana ɗan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel