Janar Abubakar a shekaru 79: Shugaba Buhari ya aike da saƙo mai daɗaɗa rai ga tsohon Shugaban kasar

Janar Abubakar a shekaru 79: Shugaba Buhari ya aike da saƙo mai daɗaɗa rai ga tsohon Shugaban kasar

  • Haifaffen ranar 13 ga Yuni, 1942, tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar ya yi bikin cika shekara 79 a duniya kuma dangi da abokai sun taya shi murna
  • Daga cikin sakonnin taya murna da aka aike wa tsohon shugaban akwai mai sanyaya zuciya daga Shugaba Buhari
  • Da yake bayyana Abubakar a matsayin fitaccen shugaba, shugaban na Najeriya ya roki Allah da ya ba shi tsawon rai
  • Shugaban majalisar dattijan, Ahmad Lawan, ya kuma aike da sakon gaisuwa ga Abdulsalam yayin da yake yi masa addu’o’i

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon gaisuwa ga tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, a yayin bikin cikarsa shekaru 79 da haihuwa.

Gaisuwar zagayowar ranar haihuwar da shugaban kasar ya aike masa yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da daya daga cikin masu taimaka masa, Garba Shehu ya wallafa a shafin Facebook.

KU KARANTA KUMA: Jigon APC ga Buhari: Ka bai wa ‘yan Najeriya canjin da suke so, ka yi maganin halin da ake ciki

Janar Abubakar a shekaru 79: Shugaba Buhari ya aike da saƙo mai daɗaɗa rai ga tsohon Shugaban kasar
Janar Abubakar a shekaru 79: Shugaba Buhari ya aike da saƙo mai daɗaɗa rai ga tsohon Shugaban kasar Hoto: AFP
Asali: Getty Images

Buhari ya bayyana Abubakar a matsayin fitaccen shugaba wanda kokarinsa na dora kasar kan turbar dimokiradiyya ke ci gaba da samar da sakamako mai kyau.

Shugaban na Najeriya ya yaba wa tsohon Shugaban kasar saboda kishin kasarsa, dattako a kan maganganun kasa da kuma yadda yake kokari a kan hadin kan kasar a koyaushe.

Buhari ya yi addu’a ga tsohon shugaban na Najeriya, inda ya roki Allah madaukakin sarki da ya ba shi karin shekaru don ci gaba da bautar Najeriya. Ya kuma yi addu’an karin hikima da ƙarfi gare shi.

KU KARANTA KUMA: Da Ɗuminsa: Gwamnan Bauchi ya naɗa Aminu Gamawa a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa

'Yan Najeriya sun gai da Abubakar

'Yan Najeriya ma sun bi sahun dangi da abokan arziki wajen taya Abubakar murna. Sashin yin sharhi na sakon Shehu ya cika da fatan alhairi, korafe-korafe da abubuwan lura. Wasu na mamakin yadda Abubakar ya girmi Buhari.

Chris Chinyere Onyeukwu ya rubuta cewa:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa Yallabai. Tarihi zai ci gaba da tunawa da kai. Da ka yanke shawarar zama matse kamar sauran mutane, amma ka yanke shawarar sake shigar da Najeriya cikin Demokradiyya."

Hameesu Adamu Ahmad ya yi tsokaci:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa ga tsohon Shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar. Da fatan Allah ya albarkaci sabon shekarunka."

Okwudịrịọnyekwuruya Ikwunemere ya tambaya:

"Wato Abdulsalami Abubakar ya girmi Buhari?"

Yakubu Musa ya lura:

"Kana nufin Abdulsalam Abubakar, da ke kasa da Buhari a rundunar soja ya girmi Buhari?"

Shugaban majalisar dattijai ya taya Abubakar murna

Jaridar The Nation ta rahoto cewa shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya taya Abubakar, danginsa, abokai da masu yi masa fatan alheri murna.

A sakon nasa na taya murna, ya yi addu'ar Allah ya kara mai bikin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya.

A cewarsa, za a tuna da Abubakar saboda nuna kishinsa ga kasa.

A wani labarin, gwamnatin Mai girma Farfesa Babagana Umara Zulum ta ce ta gabatar da ayyukan more rayuwa 556 a jihar Borno a cikin shekaru biyu da ta yi a ofis.

Jaridar Leadership ta rahoto kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Babakura Abba Jato ya na wannan bayani a ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, 2021.

Kamar yadda mu ka samu labari, Malam Babakura Abba Jato ya bayyana wannan ne wajen bikin murnar zagayowar ranar damokaradiyya a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel