Gwamnan Borno, Farfesa Zulum ya kaddamar da manyan ayyuka 556 a cikin shekaru biyu
- Gwamna Babagana Umara Zulum ya kaddamar da ayyuka 556 a jihar Borno
- Kwamishinan yada labarai na Borno ya lissafo wadannan ayyukan da aka yi
- Abba Jato ya yi wannan bayani ne wajen bikin zagayowar ranar damukaradiyya
Gwamnatin Mai girma Farfesa Babagana Umara Zulum ta ce ta gabatar da ayyukan more rayuwa 556 a jihar Borno a cikin shekaru biyu da ta yi a ofis.
Jaridar Leadership ta rahoto kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Babakura Abba Jato ya na wannan bayani a ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, 2021.
Kamar yadda mu ka samu labari, Malam Babakura Abba Jato ya bayyana wannan ne wajen bikin murnar zagayowar ranar damokaradiyya a Maiduguri.
KU KARANTA: Zan yi maganin masu kawo mana daba a siyasa - Ganduje
Farfesa Babagana Umara Zulum da ‘yan majalisar tarayya da na dokokin jihar Borno, sarakunan gargajiya, da shugabannin jama’iyya duk sun halarci bikin.
Har ila yau, wannan taro ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da jami’an tsaro da ke jihar.
Abba Jato ya gabatar da jerin ayyukan da Farfesa Babagana Zulum ya kawo, ya ce an kaddamar da 70% na wadannan ayyuka, ya ce sauran 30% suna hanya.
Kwamishinan labaran jihar yake cewa wadannan ayyuka 556 da ake magana, ba su shafi duk tsare-tsaren more rayuwa da gwamnatin Zulum ta fito da su ba.
KU KARANTA: Sakataren gwamnatin Amurka ya ce ba daidai ba ne hana mutane Twitter
A cewar kwamishinan, an yi ayyuka 194 na more rayuwa a bangaren ilmi, wadannan sun hada da gyaran wasu makarantun gwamnati a kauyuka dabam-dabam.
Har ila yau an gabatar da ayyuka 63 a bangaren sufuri, cigaban karkara da birane, sannan akwai ayyuka 59 da gwamnati ta kaddamar a aikin ruwa da muhalli.
The Nation ta rahoto Jato ya na cewa akwai ayyuka 28 da aka yi wajen samar wa matasa aikin yi, sannan an gina dakunan shan magani 74 da gidajen malaman asibiti.
A makon jiya kun ji cewa an an fara aikin titin Gwarzo zuwa Dayi, wanda zai hada jihar Kano da yankin Katsina, Zamfara, Sokoto, da Kebbi, da su ke makwabtaka.
Watanni bakwai bayan majalisar zartarwa ta kasa watau FEC ta amince da kwangilar, yanzu 'yan kwangila sun soma gyara da fadada babbar hanyar ta Gwarzo-Dayi.
Asali: Legit.ng