Da Ɗuminsa: Gwamnan Bauchi ya naɗa Aminu Gamawa a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa

Da Ɗuminsa: Gwamnan Bauchi ya naɗa Aminu Gamawa a matsayin shugaban ma'aikatan fadarsa

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya nada Dr Aminu Gamawa a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati
  • Nadin Dr Gamawa na zuwa ne bayan gwamnan ya sallami tsohon shugaban ma'aikatan Dr Ladan Salihu da wasu masu rike da mukaman siyasa a makon da ta gabata
  • Kafin nadinsa a matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Dr Gamawa ya rike mukamin kwashinan kasafin kudi da tsarin tattalin arziki na jihar Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya nada Dr Aminu Hassan Gamawa a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Bauchi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa Muktar Gidado, mai magana da yawun gwamnan ne ya sanar da nadin da ya ce zai fara aiki nan take.

Dr Aminu Hassan Gamawa
Sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Bauchi, Dr Aminu Hassan Gamawa. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sojojin Nigeria na buƙatar addu'a domin yin nasara kan Boko Haram, Janar na Sojoji

Gamawa ne tsohon kwamishina na kasafin kudi da tsarin tattalin arziki na jihar Bauchi.

A ranar Laraba da ta gabata ne Gwamna Mohammed ya sauke masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa da suka hada da sakataren gwamnati, Sabiu Baba, Shugaban Ma'aikatan Fadarsa, Dr Ladan Salihu, kwamishinoni da mashawarta 21.

Ladan Salihu shine tsohon Dirketa Janar na Rediyo Nigeria wato FRCN.

Gamawa ya fito ne daga karamar hukumar Gamawa da ke jihar Bauchi, lauya ne, malami, kwararre wurin tsare-tsaren gwamnati kuma ma'aikacin gwamnati ne.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun afka wasu unguwanni a Zaria sun sace mutane da dama

Sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnan ya yi aiki a hukumomi da maaikatu da dama, makarantu da kungiyoyin taimakawa al'umma.

A cewar sanarwar da Gidado ya fitar, Gamawa ya yi digiri na biyu da digir-gir daga Jami'ar Harvard da ke kasar Amurka.

'Yan bindiga sun afka wasu unguwanni a Zaria sun sace mutane da dama

A wani rahoton kun ji cewa Kwanaki biyu bayan harin da aka kai a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, Zaria, jihar Kaduna, yan bindiga sun sake kai hari unguwannin Kofar Gayan da Kofar Kona sun sace mutane da dama, a cewar yan sanda.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ASP Mohammed Jalinge, Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, wanda ya tabbatar da hakan ya ce har yanzu yana kan tattara bayanai domin ya sanar da yan jarida. Jama'a suna kai da kawowa a Kofar Gayan, Zaria.

Sai dai wani jami'in hukumar yan banga na jihar Kaduna, (KadVS) wanda ya yi magana da kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Lahadi a Zaria amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 12.01 zuwa 1.00 na daren Asabar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel