Jigon APC ga Buhari: Ka bai wa ‘yan Najeriya canjin da suke so, ka yi maganin halin da ake ciki

Jigon APC ga Buhari: Ka bai wa ‘yan Najeriya canjin da suke so, ka yi maganin halin da ake ciki

  • Odigie-Oyegun ya roki gwamnatin APC da Shugaba Buhari ke jagoranta da ta ba ‘yan Najeriya canjin da suka yi alkawari
  • Jam’iyyar APC, yayin yakin neman zabe a lokacin zaben 2015 ta yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin canji, shekaru shida bayan haka, har yanzu mutane ba su ga wani ci gaba ba
  • Tsohon gwamnan na Edo ya ce ‘yan Nijeriya sun dade suna son canji, kuma a matsayin ta na gwamnati “mai son ci gaba”, ya dace APC ta bai wa mutane abin da su ke bukata

Tsohon shugaban jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC), Cif John Odigie-Oyegun ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya magance hargitsi da rikice-rikicen da ke addabar Najeriya.

Odigie-Oyegun ya lura cewa shekaru shida kenan da gwamnatin APC karkashin jagorancin Buhari ta karbi mulki kuma har yanzu ‘yan Najeriya ba su ga “canjin da aka yi masu alkawari ba”, inji rahoton Daily Trust.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Bauchi ya kaddamar da shirin bada jari wa mata da matasa karkashin shirin KEEP

Jigon APC ga Buhari: Ka bai wa ‘yan Najeriya canjin da suke so, ka yi maganin halin da ake ciki
Jigon APC ga Buhari: Ka bai wa ‘yan Najeriya canjin da suke so, ka yi maganin halin da ake ciki Hoto: Aisha Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Yayin yakin neman kujera ta daya a kasar nan a shekarar 2015 da 2019, alkawuran da Buhari yayi ya ta'allaka ne kan inganta tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da rashawa.

Tsohon gwamnan na Edo ya shawarci shugaban kasar da jam’iyya mai mulki da su binciki hanyoyin dimokradiyya na magance fitinar ‘yan aware a kasar maimakon tura sojoji.

Ya bayar da shawarar ne yayin gabatar da wani littafi mai taken ‘APC’s Litmus Tests: Nigerian Democracy and Politics of Change’, a karshen mako a Abuja.

Ka magance kalubalen tsaro

Odigie-Oyegun ya nuna rashin gamsuwarsa da matsalolin tsaro na yanzu da ke barazana ga zaman lafiyar kasar.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Buhari ya ƙara muku kuɗi fiye da N700bn, ba ku da sauran uzuri, Ndume ga Sojoji

A cewarsa, magance matsalar cikin gaggawa shine zai nuna cewa APC na amsa bukatun mutanen da aka zabe ta don yi wa aiki, jaridar The Sun ta ruwaito.

Ya ce: "Abubuwa sun munana, babu tambaya. Mutane sun fusata, babu tambaya. Mutane suna jin yunwa, babu tambaya."

Tafiyar Tinubu ta na ta karfi; Magoya-baya sun dura Abuja da hotunan takara a 2023

A wani labarin, wasu masoyan jagoran jam’iyyar APC a kudancin Najeriya, Asiwaju Ahmed Tinubu, sun shigo birnin Abuja dauke da hotunan neman takararsa a 2023.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin 14 ga watan Yuni, 2021, cewa magoya-bayan tsohon gwamnan na jihar Legas sun cika gari da hotunansa.

A ranar Lahadi wadannan mutane su ka shiga lika hotunan neman takarar shugaban kasar Bola Tinubu a wuraren da aka san zai dauki hankalin jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel