Yanzu Yanzu: Buhari ya kira taron tsaro na gaggawa a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Buhari ya kira taron tsaro na gaggawa a Aso Rock

- Shugaba Muhammadu Buhari na jaggorantar taron gaggawa na tsaron kasa a fadar Villa

- Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa, ministoci, shugabannin tsaro da kuma manyan jami'an gwamnati

- Zuwa yanzu dai ba a san cikakken abunda ganawar ta kunsa ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar wani taron tsaron kasa na gaggawa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, jaridun The Nation da Daily Nigerian suka ruwaito.

Duk da cewa ba a samu cikakken bayani game da ajandar taron ba, ana sa ran yin nazari a kan halin rashin tsaro da ake ciki yanzu a sassa daban-daban na kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin kudu yan wasan barkwanci ne – Kungiyar Miyetti Allah

Yanzu Yanzu: Buhari ya kira taron tsaro na gaggawa a Aso Rock
Yanzu Yanzu: Buhari ya kira taron tsaro na gaggawa a Aso Rock Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo (SAN); Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (Rtd), na cikin wadanda suka halarci taron.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (Mai Ritaya) da kuma ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffery Onyema.

Har ila yau a cikin ganawar akwai Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; Shugaban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu; Shugaban hafsan sojojin sama, Air Marshal Isiaka Amoo; da sabon shugaban hafsan soji, Manjo Janar Farouk Yahaya.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Umahi ya yi murabus a matsayin shugaban kwamitin tsaro na Kudu maso Gabas

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba; da Darakta-Janar, Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i; Babban Daraktan Hukumar Tsaron farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, da sauran hadiman shugaban kasa su ma suna halartar taron.

A wani labarin na daban, Lai Mohammed, Ministan yada labarai na Najeriya, ya bayyana karara cewa ‘yan Najeriya da suka shiga shafin Twitter, ciki har da Fasto Enoch Adeboye, ya kamata su jira gurfanarwa.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Africa Focus a ranar Litinin lokacin da aka tambaye shi ko za a gurfanar da Mista Adeboye saboda amfani da Twitter.

Lai Mohammed ya ce: "To Babban Lauya ya bayyana a fili cewa idan wani ya karya doka, za a hukunta wannan mutumin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel